SUNAYE: Sabbin naɗe-naɗe 11 da gwamna Ganduje yayi a Kano

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya nada sabbin shugabannin ma’aikatun jihar.

Kakakin gwamna Ganduje, Abba Anwar ya sanar da haka a takarda da ya fitar daga fadar gwamnatin jihar ranar Talata.

Wadanda aka naɗa sun haɗa da:

1 – Abdalla Pakistan – Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar Kano

2 – Aliyu Musa Aliyu – Darekta Janar na Hukunar Hisba

3 – Halima Rabi’u Abdullahi – Babban Sakatariya na Hukumar Ilimi na Bai ɗaya.

4 – Gali Sadiq – Shugaban gidan Radiyon Jihar Kano.

5 – ‎Ibrahim Bichi – Babban Sakataren Ɗakin Karatu na Jihar Kano

‎6 – Sagir Sadisu Buhari – Darekta Janar na ma’aikatar Bincike da Adana.

7 – Lawan Sabo – Babban Manajan gidan jaridar ‎Triumph

‎8 – Sa’a Ibrahim – Darekta Janar gidan Talabijin din Abubakar Rimi (ARTV)

9 – Jibrilla Mohammed – Babban Manajan Kamfanin kula da kadarorin jihar Kano.

‎10 – Ibrahim Galadima – Shugaban Hukƴmar Wasanni na jihar Kano.

11 – Sakina Yusuf – Shugaban Kotun sauraren ƙararrakin matsalolin Hajji.

Share.

game da Author