Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya bayyaana sabbin shugabannin majalisar dattawa.
Ya karanta sunayen wadanda a ka nada ne a zauren majalisar dake kunshe cikin wasikun da shugabannin jam’iyyu suka mika masa.
Wadanda aka nada sun hada da,
Yahaya Abdullahi (APC, Kebbi) – Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar.
Ajayi Borrofice (APC, Ondo) – Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye
Orji Uzor Kalu – Mai tsawatarwa na Majalisa
Aliyu Abdullahi (APC, Niger) – Mataimakin Mai tsawatarwa
Enyinnaya Abaribe (PDP)- Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisa
Emmanuel Bwacha (PDP, Taraba) – Mataimakin shugaban Marasa Rinjaye.
Philip Aduda – Mai tsawatarwa na Marasa Rinjaye
Sahabi Yau (PDP, Zamfara) – Mataimakin Mai tsawatarwa na Marasa Rinjaye
Discussion about this post