SUNAYE: Jihohi da kananan hukumomin da za su iya fadawa matsalar amai da zawo a kasar nan

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta lissafo jihohi da kananan hukumomin da cutar amai da gudawa zai addaba idan ba a maida hankali ba.

NCDC ta gano haka ne a bincike da ta gudanar da hadin guiwar ‘eHealthAfrica’ inda ta bayyana cewa jihohin Kano, Kebbi da Sokoto na cikin jihohin da za yi fama da wannan matsala idan ba ayi gaggauta daukan mataki a kai ba.

Hukumar ta ce sakamakon wannan binciken zai taimaka wajen fadakar da gwamnatocin jihohin kasar nan wajen maida hankali game da cutar.

JIHOHIN DA KANANAN HUKUMOMI

1 – Kano State – Wudil, Kiru, Gwarzo, Karaye, Shanono, Bagwai, Kabo, Rimin Gado, Tofa, Madobi, Gaya, Dawakin Kudu, Fagge, Ungogo, Bichi, Dawakin Tofa, Tudun Wada, Garun Malam, Bebeji, Rano, Bunkure, Kibiya, Doguwa, Gezawa, Rogo, Kumbotso, Kura

2 – Kebbi State – Aleiro, Argungu, Gwandu, Augie, Maiyama, Suru, Koko-Besse, Dandi, Birnin-Kebbi, Jega, Kalgo, Bunza, Ngaski, Yauri, Shanga

3 – Sokoto state – Tambuwal, Bodinga, Binji, Yabo, Sokoto South, Wamakko, Dange, Shuni, Sokoto North, Kware, Silame, Kebbe, Shagari, Tureta, Rabah

4 – Borno State – Jere, Monguno, Biu, Kwaya, Kusar, Bayo, Hawul, Damboa, Askira/Uba, Dikwa, Mobbar

5 – Zamfara State – Gusau, Bakura, Gummi, Bukkuyum, Anka, Maru, Talata, Mafara, Maradun, Birinin, Magaji-Kiyaw, Zurmi

6 – Kaduna State – Igabbi, Zaria, Kaduna south, Soba, Ikara, Kudan, Makarfi, Sabon Gari, Kauru, Kubau

7 – Bauchi state – Bauchi, Jama’are, Dass, Bogoro, Tafawa -Balewa

8 – Nasarawa state – Akwanga, Toto, Obi

9 – Yobe State – Gujba and Gulani

10 – Kwara state – Ilorin west and Ilorin East

11 – Niger state – Agwara and Magama

12 – Kastina state –Danja

13 -Taraba state – Ibi

14 – River State – Andoni

15 – Plateau State – Jos North

16 – Benue – Markurdi

CUTAR KWALARA

Cutar amai da zawo ko kuma kwalara cut ace da ake kamuwa da ita a dalilin yin amfani da ruwan da bashi da tsafta,rashin tsaftace muhalli, rashin wanke hannu bayan an yi amfani da ban daki, yin bayahaya a waje da sauran su.

Alamun cutar sun hada da Zazzabi, mai da gudawa,rashin jin karfi a jiki, rashin iya cin abinci, suma da sauran su.

HANYOYIN GUJE WA KAMUWA DA CUTAR.

1. Tsaftace muhalli.

2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.

3. A guji yin bahaya a waje.

4. Amfani da tsaftattacen ruwa.

5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.

6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.

7. Yin allurar rigakafi

8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.

Share.

game da Author