Fadar Shugaban Kasa ta turo wa PREMIUM TIMES sanarwar nada sabbin hadiman Shugaba Muhammadu Buhari su 11.
An sake nada su ne makonni biyar bayan sake rantsar da Buhari domin sake shafe shekaru hudu a kan mulki.
SUNAYEN SABBIN HADIMAI 11 DA SHUGABA BUHARIN YA SAKE NADAWA
1. Mohammed Sarki Abba – Babban Hadimin Shugaban Kasa Kan Harkokin Gida Da Tsara Taruka
2. Shehu Darazo – Babban Hadimin Shugaban Kasa Kan Ayyukan Musamman
3. Dr Suhay Sanusi Rafindadi – Likitan Shugaban Kasa Na Musamman
4. Amb. Lawal A. Kazaure – Shugaban Tsara Ayyukan Shugaban Kasa
5. Sabiu Yusuf – Hadimi Na Musamman (Ofishin Shugaban Kasa)
6. Saley Yuguda – Hadimin Shugaban Kasa Na Musamman (Kula Da Tsaftar Gida)
7. Ahmed Muhammed Mayo – Hadimin Shugaban Kasa Na Musamman (Harkokin Kudade Da Gudanarwa)
8. Mohammed Hamisu Sani – Hadimi Na Musamman (Ayyukan Musamman)
9. Friday Bethel – Hadimin Shugaban Kasa (Ayyukan Yau Da Kullum)
10. Sunday Aghaeze – Hadimin Na Musamman (Mai Daukar Shugaban Kasa Hotuna)
11. Bayo Omoboriowo – Hadimi Na Musamman (Mai Daukar Shugaban Kasa Hotunan Musamman)
Sanarwar wadda Babban Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya saw a hannun, ta ce aikin na su ya fara ne tun daga ranar 29 Ga Mayu, 2019.