Su waye matsalar Arewa, Masu Kudi ne, Masu mulki, Sarakuna ne ko Talakawa? Daga Mohd Ibn Mohd

0

A lokutta da dama na kan shiga cikin tunani mai zurfi domin gano ko su waye ainihin matsalar Arewacin Najeriya, Masu Kudi ne, Masu mulki, Sarakuna ne ko Talakawa.

Idan dai ka na hira da mai kudi, wanda Allah yayi wa rufin asiri wato yana cikin daula, zaka ji yana yawan fadi cewa Talakawa sune matsalar yankin Arewa.

Shugabannin na gwamnatoci suma a kullum za su yi magana, a kan talaka ya ke karewa, sannan su kansu sarakuna da dattijan gari basu bar talaka ba sai dai sun fi tausaya musu ne kawai.

To wai shin wanene matsalar Arewa a Najeriya?

Masu Kudi

Shi dai mai kudi musamman a Arewacin Najeriya bashi da makiyi irin Talaka. A kullum dada nesanta kansa yake yi da Talaka. Yana ganin idan ya bari Talaka ya cika matsarsa zai iya sa ya talauce .

Baya ga su kansu, matansu da yayan su ma duk haka suke. Su da kansu sun kirkiro makarantun kudi domin ‘ya’yan su.

Duk inda kaga makaranta ta gwamnati musamman ta Firamare zaka ga na ‘ya’yan fukara’u ne bayin Allah.  Sannan malaman da ake turawa su karantar dasu ma basu damu da su ba. Tun safe zaka ga yaro yana galantoyi a harabar makaranta malaman kuma na karkashin itace suna hira zuwa lokacin tashi yayi.

Masu hali kuwa ‘ya’yan su na can makarantun kudi ana karantar dasu.

Kiyayya tsakanin masu kudi da Talaka ya yi zafi yanzu domin harta unguwanni zaka ga ana kekkebe wa idan har ya zama dole sai an zauna kusa da juna sai a girke jami’an tsaro a gida bayan gina dankareren katanga da suka kewaye gidajen su da shi.

Sarkuna

A zamanin da sarakuna ne gatan talaka duk wani abu da ya taso na matsalar gida ne ko gona ko kuma auratayya, zaka ga gabadaya wurin sarki ake dunguma a tafi.

Sarakuna sune ke yi wa al’umma iso ga gwamnati. Sune kusan ke ciyar da talakawan su. Gatan talaka Sarki.

Sai dai kuma kash, yanzu abin duk ya canja, suma sarakuna sun fara nesanta kansu da talakawa. Muamulolunsu kaf ya koma sai da masu kudin gari da gwamnati. Tsakaninsu da talaka sai cuta da handame musu dukiyoyi.

A wasu kauyukan zaka ga sarki na kwace wa Talakawan sa gonaki, gidaje kai har matayen su ma da sunan shi sarki ne mai iko. Sau dayawa ana kai ruwa rana tsakanin sarakunan kauye da talakawan su a dalilin irin haka.

Masu Mulki

Su ko Masu Mulki sune suka fi zama matsalar Talaka. Mutum a kan mulki wanda talaka ya jajurce, ya uni a layi, wasu ma suka rasa rayukansu a dalilin mutum ya zama shugaban Kasa, Gwamna, da dai sauransu. Amma da zaran sun dare kujerar mulki sai kaga komai ya canja ba talaka bane kuma a gaban sa.

Yau ko koda dan talaka ne ya zama wani abu sai kaga idan ba wani ikon Allah ba sai ya canja ya sakala kansa cikin shima wai yanzu attajiri ne.

Sai ya yakice wadanda yake tare dasu ada ya koma unguwannin masu kudi wai shima ya kudance.

Abinda aka tura shi yayi ba zai yiba sai dai kawai Iyalansa da wasu daga cikin ‘yan uwansa da Allah ya ci da su.

Talakawa

Babu yadda za ace wai talaka ya gyaru idan ba gwamnati ta waiwayeshi bane, Mai kudi ya karkato zuwa gareshi haka suma sarakuna suna dubin su akai-akai.

Kyale su da aka yi ne ya, kowa ya ce ko-oho shine yasa ake fama da su ana rika cewa talakawa ne matsala.

Ina Talaka yake da matsala bayan kun danne abubuwan da yakamata ya kai garesu. Yana wahala yana ganin kuna cikin daula da kudaden gwamnati.

Mai kudi zai iya juya Talaka da kudin sa, Sarakuna da ikon su, gwamnati kuma da karfinta amma an kyale su dole ko watarana su yi wa kowa bore.

Lallai idan ba azo an zauna an kirkiro hanyoyin da za a rika agaza wa talaka ba wanda shine yake haihuwa ‘ya’yansa suke tagayyara, suna galantoyi a tituna saboda rashin iya kula da su wata rana da kujerar gwamnatin da na sarakunan da kai da kudin ka sai ya gagareka juya wa ko zama a kai.

A kullum dole a rika sara ana duban bakin gatari. Ya’yan talakawa suma a rika basu daman shiga irin wadannan makarantu da masu kudi ke saka ‘ya’yan su idan gyara ta gwamnatin zai yi wuya.

A harkar kasuwanci masu kudi su rika jawo su kusa sna agaza musu dan ko ba haka ba akwai sauran rina a kaba.

Share.

game da Author