Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta kada sabuwar bataliya a Daura, garin da aka haifi Shugaba Muhammadu Buhari.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an kafa Bataliya ta 171 a Daura, domin su rika sa ido a kan mahara daga bangaren kan iyakan Arewacin kasar nan ta Jihar Katsina, inda aka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Majiya a cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa bataliyar za ta taya Rundunar Mayaka ta 17 ta Sojan Infantry da kuma kuma Bataliya ta 35 da ke cikin Katsina, babban birnin jihar.
Wannan bataliya da za ta kasance a karkashin wani Laftanar Kanar, daban ta ke da Rundunar ‘Fort Muhammadu Buhari’, ta wasu zaratan sojoji da aka kafa tun cikin Mayu, 2017 a Daura. Ita wannan din a karkashin Bataliya ta 35 ne aka kafa ta tun cikin 2017.
A yanzu Bataliyar Katsina ta 35 da wannan sabuwa ta 171 da aka kafa a Daura, duk za su kasance ne a karkashin Hedikwatar Sojan Infantry da ke garin Katsina.
Tun bayan da Buhari ya zama shugaban kasa matsalar tsaro ta kara tabarbarewa a Jihar Katsina da sauran jihaohin da ke makwabtaka da ita.
Tuni da aka bada odar cewa bataliyoyin sojojin da ke fadin kasar nan su yi karo-karon sojoji, a hada bataliya guda mai karfi ta zaratan sojojin da za a tura Daura, su 350.
Da PREMIUM TIMES ta tambayi Kakakin Yada Labarai na Hedikwatar Tsaron Kasa, sai Onyema Nwachukwu ya ce wannan tambayar Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya kamata ya amsa tambayar.
Sai dai kuma har zuwa yau Laraba da rana, Musa bai amsa wannan tambaya ba.
Cikin shekaru uku daga 2016 zuwa yanzu, an kafa bataliyoyin soja a jihohi daban-daban domin kokarin dakile hare-haren ta’addanci da da ‘yan bindiga masu garkuwa da satar shanu da fadace-fadacen makiyaya da manoma.