Babbar Jama’iyyar adawa, PDP, ta tsaya kan bakan ta cewa ba ta amince da Elumelu ba, ta ce sai dai Hon. Kingsley Chinda ne zai zama shugaban marasa rinjaye.
Sakataren Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa su dai ba su san da zaman Elumelu ba, sai Chinda shi ne Shugaban Marasa Rinjaye.
Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajamiamila ne ya bayyana sunan Elumelu a matsayin Shugaban Masara rinjiye, duk kuma da cewa ba shi ne ita PDP din ta amince a bai wa shugabancin ba.
Gbaja ya ambaci sunan Elumelu dan asalin Jihar Delta da kuma Toby Okechukwu a matsayin shugaba da mataimaki na marasa rinhaye. Sai kuma Gideon Gwani da Adesgun Bulaliyar Majalisa da kuma Mataimakin Bulaliyar Majalisa.
Wannan ya sa mambobin PDP sun yi ta tayar da hargitsin cewa ba su amince ba, kuma nan take suka bayyana sunan wanda su ke so, wato Chinda.
Mambobin PDP sun nuna bacin ran su da Kakain Majalisar, Gbajabiamila, saboda ya shigar da sunayen da ba su ne aka ba shi a matsayin wadanda za su rike mukamai a majalisar tarayya ba.
Wannan cushen sunaye da Gbajabiamila ya yi ya haifar da hargitsi da kuma rincimi a majalisar, a jiya Laraba, har sai da wasu suka bai wa hammata iska.
Discussion about this post