Shugaban Alkalan Kotun Daukaka Kara, Zainab Bulkachuwa ta soke tafiya hutun dukkan alkalan da ke shari’un da da suka shafi kararrakin zaben 2019.
Tun a ranar 8 Ga Yuli ne alkalan Babbar Kotun Tarayya suka fara hutun su na shekara-shekara, yayin da wasu kuma za su fara a yau Litinin, 15 Ga Yuli.
A cikin wata sanarwa da jami’ar yada labarai ta Kotun Daukaka Kara, Sa’adatu Musa-Kachalla ta sa wa hannu, ta bayyana cewa hana alkalan tafiya hutu na da nasaba ne da yawan tulin shari’un zaben 2019 da ke a gaban su.
Bulkachuwa ta ce tunda akwai adadin rana da kwanakin da aka gindaya cewa za a kammala dukkan shari’un a cikin su, to akwai bukatar yin azama cikin hanzari a kammala shari’un, don kada tafiya hutun alkali ya kawo cikas.
“Tilas sai mun sadaukar da hutunmu na shekara-shekara domin samun kammala dukkan shari’un a cikin lokaci.” Haka Bulkachuwa ta bayyana a cikin sanarwar.
Bulkachuwa ta kara da cewa da tsallaken tsawon kwanakin da za a yi ba a gudanar da shari’u ba, saboda tafiyar alkalan hutu, zai shafi iyar wa’adin da aka tsara za a kammala shari’un.
Amma kuma Bulkachuwa ta kara da cewa ta umarci dukkan alkalan da suka tsara yin amfani da lokutan hutun domin su tafi neman maganin rashin lafiya, ko kuma magance lalurorin gida na tilas, to su rubutu a ba su iznin tafiya hutun da bai wuce kwanai 15 ba.
An ce ta na so a tsara yadda ba za a rasa alkali uku a kotun da wani alkali ya tafi hutun neman lafiyar sa ba tsawon kwanaki 15, wadanda za su saurari shari’un da ake gudanar wa.
Sanarwar ta fayya ce cewa alkali daya ne aka amince ya tafi hutu, daga cikin alkalan da ke zaman sauraren kowadanne kararrakin zabe a kasar nan.
“Ta ce amma sai alkali biyar daga Kotun Daukaka Kara ne za su iya zaman sauraren kararrakin zaben gwamna.
Ta kawo hujjar cewa akalla akwai kararrakin da suka shafi shari’un zabe har 800 ya zuwa 17 Yuli, 2019.
Wannan bayani na adadin yawan kararraki, ya fito ne daga ofishin Mataimakiyar Rajistara ta Kotun Daukaka Kara, Rabi Yakubu.
Ya zuwa yanzu dai kararraki 65 kadai aka saurara, wasu kuma aka kore su a kotunan daukaka kara daban-daban.
Akwai kotuna 77 da aka kafa domin sauraren kararrakin da suka shafi zaben 2019.
Daga cikin kararraki 800, akwai 415 na tankiyar zaben Majalisar Dokoki ta Jiha daban-daban. Akwai kuma guda 105 na rashin amincewa da zaben sanata da wasu suka kai karar. Sai zaben Majalisar Tarayya kuma akwai 214, na gwamna guda 62, na shugaban kasa kuma guda 4.