SHARI’AR ZABE: Buhari ya nuna rashin yarda a gabatar da takardun ilmin sa a kotu

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amin cewa a yi amfani da bayanan takardun makarantar sa a Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa.

Babban Lauyan Buhari, Wole Olanipekun ne ya nuna kin amincewar a jiya Litinin lokacin da ake ci gaba da sauraren karar zaben nasa, wadda Jam’iyyar PDP da dan takarar ta, Atiku Abubakar ya suka kai kotu.

Daga cikin abin da PDP za ta gabatar wa kotu, har da takardun bayanan iya zurfin ilmin da Buhari ya hada a cikin fam na INEC mai lamba CF001, wanda PDP ke kalubalantar cewa babu wasu takardun kammala shaidar karatun sakandare na Buhari.

Kuma daga cikin hujjojin rashin cancantar sa tsayawa takarar da PDP da Atiku ke tinkaho, har da abin da wannan fam mai lamba CF001 ya kunsa.

Shi wannan fam duk bayanan da ke cikin sa, da kuma takardun da aka hada aka bayar wa INEC tare da shi, da su ne ake tabbatar da cancantar tsayawa takara, ko kuma rashin cancantar tsayawar dan takara zabe.

Da ya ke Buhari bai bayyana wasu bayanai na takardun kammala sakandaren sa a cikin fam din ba, dalili kenan wasu ‘yan Najeriya da dama ke cewa bai cancanci tsayawa takara ba.

Wannan dalili ko hujjar da wasu ke kafawa ce ita ma jam’iyyar PDP ke amfani har da ita wajen kalubalantar tsayawa takarar Buhari zaben 2019 da aka gudanar cikinn watan Fabrairu.

Can a Kotun Daukaka Kara kuma ana jiran ranar da za a yanke hukunci a kan cancanta ko rashin cancantar Buhari tsayawa takara, a karar da wasu mutane uku suka shigar kan Buhari, INEC da kuma jam’iyyar APC.

APC taki amincewa a gabatar da batun Takardun Buhari

Jam’iyyar APC wadda Buhari ya tsaya takara a karkashin ta, ta ki amincewa da a gabatar da batun fam CF001 a Kotun Daukaka Kararrakin Zabe, Ta bayyana wa Alkalai masu shari’a cewa za ta fadi dalilan ta na kin amincewa da batun.

Sauran takardun bayanan da aka gabatar wa kotu a matsayin shaidu a jiya Litinin, har da kwafe-kwafen wasu bayanai da aka buga a wasu jaridun kasar nan, sai kuma kwafe-kwafen takardun sakamakon zabe.

Tuni dai jam’iyyar PDP ta gabatar da kwafen takardun bayanai guda 26,235 a kotu. Sannan kuma ta kara da kwafe-kwafen sakamakon zabe har guda 6,806 duk a kokarin ta na kafa hujjar cewa an tafka magudi kamar yadda ta yi zargi.

A jiya Litinin kuma PDP ta gabatar da shaidu na mutane shida a kotu.

Share.

game da Author