SHARI’AR ZABE: Atiku ya gabatar da Buba Galadima yin shaida a kotu

0

Jam’iyyar PDP ta gabatar da tsohon na hannun damar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai shaida a Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Shugaban Kasa, da aka fara tafka shari’a a Abuja.

PDP da Atiku sun kai kara ne, inda suke kalubalantar nasarar da INEC ta bayyana cewa Buhari da APC ne suka yi. Atiku da PDP sun ce su ne suka yi nasara, ba Buhari da APC ba.

Galadima wanda dan baya dan ra’ayin rikau ne na takarar Buhari a tsakanin 2003 har zuwa 2011, ya shaida wa kotun cewa kotun a baya cewa ya raba hanya da Buhari, saboda shi Galadima din ya yi amanna cewa Buhari ya kasa cika alkawurran da ya daukar wa jama’a kafin a zabe shi a lokacin da ya ke kamfen.

Buba Galadima, wanda ya yi wa Atiku Daraktan Kamfen na Yada Labarai a lokacin zaben 2019, sai da jami’an tsaro suka tsare shi a lokacin da ake gudanar da zaben shugaban kasa na 2019.

A lokacin da lauyoyin APC ke masa tambayoyi, Galadima ya musanta zargin da suka yi masa cewa ya fice daga APC saboda Buhari bai ba shi mukamin komai ba.

PDP ta gabatar da Galadima bayan ta mika takardun sakamakon zabe daga jihohi 10, wadanda ta ce su na daga cikin shaidun ta da ke nuna cewa an tafka magudi zaben, wanda ta ce an sheka wa Buhari aringizon kuri’u.

Share.

game da Author