Shari’ar El-Zakzaky ba a hannun Buhari ta ke ba –Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa shari’a ko tuhumar da kuma ci gaba da tsarewar da ake wa Shugaban Mabiya Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, ba laifin shugaban kasa ba ne.

Sanarwar ta ce malamin ya na fuskantar tuhuma a Kaduna. Don haka kada ma a dora wa gwamnati cewa ita ke da laifin ci gaba da tsare shi.

Kakakin Shugaba Muhammadub Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a jiya Juma’a, a cikin wata takardar da ya fitar wa manema labarai.

Mabiya El-Zakzaky na ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoran na su, kamar yadda kotu ta yi umarni a baya.

A jiya Juma’a sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, inda suka bijire wa ka’idar takaita zanga-zanga a dandalin Unity Fountain kadai, kamar yadda jam’ian ‘yan sanda suka yi gargadi a farkon wannan mako.

Malamin ya na fuskantar shari’a ne a Kaduna, sanadiyyar rikicinn da ya biyo bayan tare hanyar da mabiyan sa suka yi wa sojoji a cikinn watan Disamba, 2015.

Wannan ya haifar da mummunan kisan da sojoji suka yi wa mabiyan sa a lokacin.

Shi ma an ji masa ciwo tare da matar sa Zeenat sanadiyyar harbin da ya samu bayan da aka kai wa gidan sa hari.

Sannan kuma an kashe masa ‘ya’ya uku a lokacin mummunan rikicin.

Duk da umarnin da kotu ta bayar, har yau ba a sake shi ba saboda wasu dalilai wadanda a baya gwamnatin tarayya ta bayyana.

Sai dai kuma a jiya Fadar Shugaban Kasa ta shawarci mabiya malamin da su daina fitowa kan titina su na tayar da hankulan jama’a domin neman a saki jagoran su.

Garba Shehu ya bayyana cewa kamata ya yi su maida hankali a kotu inda a ke ci gaba da shari’a, domin batun sa ya na kotu, ba a hannun shugaban kasa sa.

Ya ce mabiya malamin ba su da wani izni ko fifikon fitowa sun a yadda suka ga dama tare da take doka da sunan zanga-zanga.

Ya ce wadanda suke takurawa a lokacin zanga-zanga, ta hanyar tare hanyoyi, su ma su na da ‘yancin yin zirga-zirga, ba tare da wani ya tare musu hanya ba, kamar yadda mabiya malamin ke yi.

Sanarwar ta kuma kara da cewa ba fa kowace gwamnati ba ce za ta iya zura ido ta na kallon yadda wasu ke lalata dukiyoyi da kawo wa zamantakewar wasu masu bin doka da oda barazana da sunan zanga-zanga.

Ya ce Shugaba Buhari ba ya yi wa kotu katsalandan cewa a saki wani ko a daure wani.

Daga nan ya ce su bi ba’asin shari’ar El-Zakzaky a kotu, ba hannun Buhari ba, tunda ba Shugaban Kasa din ne ya tsare shi ba.

Share.

game da Author