Gidauniyar Bill Gates da Dangote sun jadadda cewa za su ci gaba da tallafa wa Najeriya wajen yaki da kawar da cutar shan inna a ƙasar.
Bill Gates da Dangote sun bayyana haka ne a hiran da suka yi da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ta wayar tarho ranar Asabar.
Mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai Abba Anwar ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Anwar yace Dangote da Bill Gates sun yaba wa Ganduje bisa namijin kokarin da yakeyi wajen inganta kiwon lafiyar jama’ar jihar.
Sun ce suna sa ran samun sakamako mai kyau a dalilin hada hannun da za su yi da gwamnati wajen kawar da cutar shan inna a jihar.
Bayan haka shugaban cibiyar kiwon lafiya a matakin farko na jihar Tijjani Hussaini ya bayyana cewa gwamnati ta dauki wasu matakan inganta fannin kiwon lafiyar jihar.
“ Mun hada hannu da manya manyan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin samar da hanyoyi masu sauƙi da cibiyoyin kiwon lafiya za su iya aikawa da marasa lafiya da suka gagaresu zuwa wasu asibitocin.
Bayan haka Bill Gates ya yabawa nasarorin da aka samu wajen kawar da shan inna da gwamnati ta yi a jihar Barno duk da yadda ake fama da hare-haren Boko Haram.
Mai taimakawa gwamnan jihar Isa Gusau ya bayyana haka a Maiduguri ranar Juma’a.
Gusau yace Bill Gates ya bayyana cewa hada hannun da ma’aikatan kiwon lafiya ta yi da sojojin Najeriya ya sa an sami nasarar yi wa yara allurar rigakafi a wuraren dake da wahalar zuwa a jihar.
Gates ya kuma yi murna matuka bisa yadda gwamnan jihar Babangana Zulum ya saka cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a matakai 10 na samar da ci gaba da ya tsara a jihar tun bayan rantsar dashi da akayi.
Ya kuma ce Zulum ya kuma yabawa tallafin da Dangote ya riƙa turawa jihar musamman a wajen inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.
Zulum ya lissafo kadan daga cikin tallafin da jihar ta samu daga gidauniyar Bill Gates wanda ya hada da samar da abinci, magunguna da kayan sawa
na tsawon shekaru uku sannan da kayan gini da gidauniyar Dangote ta riƙa aika mana domin gine-gine da muke yi domin samar wa mitane matsuguni.
Gusau yace Zulum ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnati zata fara gina cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda bakwai a kananan hukumomin Hawul, Gwoza, Kala-Balge, Askira-Uba da Jere.