Abun ya fara zama INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN, dole sai an tashi tsayin-daka anyi fada da wannan musibar, ba abun da za a dinga yayatashi bane a dandalin sada zumunta.
Tun muna hango abun daga nesa, yanzu yazo har cikin gidajenmu da dakunanmu. Wai me yake damun wasu matan ne? Anya kuwa, Allah ya kiyaye. Idan har mace zata dauki makami ta kashe mijinta, babu shakka zata iya yin komai.

Duk mutumin da ya kashe mu’umini da gaske idan ya shiga wuta ba zai fita ba saidai Allah ne yaso. Balle kuma wacce taci amanar aure ta kashe mijinta, wannan ai cin amana ne.
Ahirrr dinku mata wallahi, shaidan zai kaiku ya baroku, ko a cikin matan kafirai sai jahilar gaske ce zata iya kashe mijinta balle musulma wacce take yin kalmar shahada.
Allah ya tsaremu da aikin da-na-sani, kin kashe mijinki, a yayin da kuke da yara uku, gashi kuma zaki tafi kurkuku kiyi rayuwar wahala. Sannan ‘ya’yanki me zaki ce musu idan sun tambayeki a kurkuku? Don dole su dinga kai miki ziyara idan har ba a kasheki ba kamar yadda muka saba gani.
Ban ce maza basa laifi ba, kuma ba goyon bayansu nake ba, amma rashin tarbiya ne zaisa ki jefi mijinki koda da kofin shayi ne balle kuma ki caka masa wuka.
Shiyasa akeso mutane su dinga nutsuwa wajen neman aure saboda ba kowacce mara kan-gado ake aure ba. Annabi (SAW) yace, ku auri mu’umina, ma’abociyar addini ba yar jagaliya ba.
Rashin bin umarnin Annabi (SAW) ne yake bamu wahala a rayuwar aure.
An sauka daga tsarin tafiyar ne yanzu, an koma yin auren bariki da yahudanci. Shine dalilin da yasa ake ta ganin sa6ani, dama Manzon Allah (SAW) yace, duk wanda ya biyo bayansa zai ga sa6ani iri iri.
Wani abun mu muke jawowa kanmu, idan bamu daina auren dole, auren bariki da auren kwadayi ba, dole a samu matsala. Duk macen da ka aurota cikin tarbiya, soyayyarka, da tsoron Allah kuma ka kiyaye hakkinta, ko pencil ba zata iya tsira maka ba insha Allah.
Ni, Comrade Soron Dinki (Garkuwar matasan Arewa), ina kalubalentar gidajen yada labarai da suke bayyana irin wadannan labarun ba tare da bayyana hukuncin da yake biyo baya ba. Shiyasa abun yake arha a wajen mata bata gari.
Babban kalubalen da irin wadannan mata masu kashe miji suke samu shine, idan har ma ba a kashesu ba, suna samun kansu a cikin nadama, cikin wulakanci a kurkuku da rashin shakar iskar ‘yanci irin na ragowar mata.
Fatara da talauci da yunwa ne zasu damesu, sannan babu su babu miji tunda a tsare suke. Daga sanda kuka aikata laifin kun shiga bala’i saboda bakin mutane ma ya isheku. Watakila, a baya kina cikin jin dadi, yanzu kuma kin koma cin garau-garau a kurkuku har ki mutu idan anyi miki daurin rai-da-rai.
Babu abun da zai kashe mana jiki a rayuwarmu da matanmu, idan muka yi niyar aure zamu yi, idan kuka yi laifi dole zamu nuna muku kuskurenku tunda a kasanmu kuke. Maganar ajje wuka a gida ya zama wajibi, dole sai mata sun ajje zafin kai a gefe sun bi shugabannin da Allah ya kafa musu.
Allah ya shiryar damu.