Sanata Lado ya karyata labaran da ake yaɗawa game dashi a kafafen yaɗa labarai

0

Malam Ibrahim Khalil, Mataimaki na musamman ga tsohon sanata Bashir Garba Lado, ya mayar da martani ga wata kungiyar siyasa daya zarga da cewa ta himmatu wajen ganin ta batawa tsohon sanatan suna sakamakon hamayyar siyasa da yace wasu marasa tarbiya sun yi amfani da wata kafar sadarwa ta yanargizo wajen kirkirar sharri da kage domin kawo cikas ga siyasar sanatan tare da haddasa fitina a cikin jamiyyar APC.

Sanata Bashir Garba Lado ya shiga jamiyyar APC ne bayan ya gamsu da kyawawan manufofin ta da gamsuwa da adalcin Shugaba Muhammadu Buhari, ba kamar yadda masu hammayya dashi suke ikirarin cewa jamiyyar APC tayi masa wasu alkawura domin lallashin sa kan bukatar sa ta takarar sanata ba.

Ibrahim Khalil yace duk wanda yasan Sanata Lado, yasan irin wadancan kalamai ba irin halinsa bane, don shi mutum ne mai imani, da rungumar kaddara wajen sha’anin mulki don haka bashi da abokin jayayya a harkokin sa na siyasa.

Kuma suna sane sarai cewa irin wannan sharri da kage ba zai tsaya iya kan Sanata Ladon ba, suna da labarin cewa akwai wasu bayan shi da irin wannan sharri zai shafa, da sannu zasu gurfanar da wadanda suka kulla wancan sharrin gaban kotu domin abi masa hakkin sa, ciki harda kafafen da suka bada damar cin zarafin sanatan.

Sanata Lado bai yi hira da wani dan jarida na gida ko na kasashen ketare ba.

Matsayin Sanata Lado shine jaddada godiya ga Allah da shugaba Muhammadu Buhari, da shugabancin jamiyyar APC na kasa da na jiha.

Allah ya karawa shugaban kasa da jamiyar mu ta APC nasara.

Share.

game da Author