Samar da inshorar kiwon lafiya ga kowa-da-kowa a Najeriya ne mafita – Inji Kungiyar Likitoci

0

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA) Francis Faduyile roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tilas ta wa hukumar Inshorar Kiwon Lafiya ta Kasa ta saka duk ‘yan Najeriya a shirin Inshorar kiwon Lafiya ta kasa.

Ya ce hakan ne kadai hanyar da tabbatar wa ‘yan Najeriya da kiwon lafiya mai nagarta.

“ Sanin kowa ne cewa talaka a Najeriya na fama da matsalar rashin kudin asibiti wanda da dama sai dai abi ta wani hanyar amma wajen samun magani a kasar nan.

Idan ba a manta ba kwanakin baya ne mutane musamman ma’aikatan kiwon lafiya suka yi ta korafin rashin more shirin inshorar kiwon lafiya a kasar nan inda a dalilin haka ne gwamnati ta amince ta sake duba dokar kafa shirin.

Bayanai sun nuna cewa majalisar dokoki ta kasa ta kammala duba dokar sannan har ta aika wa shugaban kasa rahotonta.

Bayan haka Faduyile ya kuma yi kira ga shugaban kasa kan karfafa aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan sannan da bude bankunan da ma’aikatan kiwon lafiya za su iya karban bashi domin siyo kayan aikin da suke bukata.

Ya kuma yi kira ga Buhari da a rage harajin da ake karba a kayan aikin asibiti idan za a shigo da su kasar nan.

“Muna kuma bukatan gwamnati ta karkato da hankalinta wajen samar da tsaro a kasar nan sannan da kara wa fannin kiwon lafiya kaso mai tsoka a kasafin kudin kasa.

A karshe Faduyile yace kungiyar NMA za ta ci gaba da hada hannu da gwamnati domin samar da ci gaba a kasar nan.

Share.

game da Author