SABON HARI: ’Yan bindiga sun kashe mutane 29 a Kauyukan Sokoto

0

Wasu ’yan bindiga sun kai hare-hare a cikin wasu kauyukan da ke karkashin Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane 29.

Ya ce Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Sokoto Ibrahim Ka’oje ya yi alkawarin gaggauta kara matsin-lambar tsaro a jihar.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara yankunan da mahara suka yi kashe-kashen.

Harin wanda aka kai a ranar Laraba da ta gabata, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Sokoto ya tabbatar da shi, kuma ya ce an kashe mutane da yawa, inda ya kira makasan da suna “wasu mahara marasa imani.”

Shi kuma Shugaban Riko na Karamar Hukumar Goronyo, Zakari Chinaka, ya shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Juma’a cewa ‘yan bindigar sun banka wa shaguna wuta, kuma sun saci shanu.

Ya ce maharan sai da suka shafe awa biyu cur su na barnar su yadda suka ga dama, saboda akwai matsalar tsaro a yankin.

Kauyukan, kamar yadda Chinaka ya bayyana, su na da tazarar tafiyar mota ta tsawon awa uku tsakanin su da Sokoto, babban birnin jihar.

Sannan kuma ya ce a lungu su ke, shi ya sa su ke da wahalar kai musu dauki a irin wannan mawuyacin lokaci.

Chinaka ya ce an kashe mutane 23 a kauyen Kamitau, wasu biyar a kauyen Ololo, sai kuma mutum daya da aka kashe a kauyen Rijiyar Tsamiya.

“Allah ne kadai zai iya rama wa jama’ar da suka yi asarar dukiyoyin su. Saboda an kona musu rumbuna, shaguna, kuma an sace dukkan shanun da ke yankunan kauyukan uku.”

Wani mazaunin Goronyo mai suna Shafiya’u, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an bar gawarwakin wadanda aka kashe zube, saboda jama’a da kuma jami’an tsaro ba su iya shiga lungun da aka yi kisan da wuri ba.

“An fi kashe jama’a da dama a kauyen Kamitau, saboda al’ummar garin sun yi gangami su ka bi mahara a guje da nufin kwato shanun su da aka kwace. Amma kuma sai aka samu akasi, da suka kure wa ‘yan bindigar gudu, sai suka bude musu wuta, har suka yi musu mummunan kisa.’ Inji Shafaya’u.

Wata majiya ta ce masu harin sun dira wajen karfe 5 har zuwa 7 na dare. Kuma sun hakkake cewa daga cikin Jamhuriyar Nijar su ka shigo.

Limamin masallacin Izala na Goronyo, Isma’il Sani, ya yi kira a lokacinn hudubar sa ta ranar Juma’a cewa gwamnati ta tashi tsaye domin ta hana sake zubar da jinin jama’a haka nan.

Share.

game da Author