Tun daga lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya karanta jerin sunayen sabbin ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya tura majalisa domin amincewa, al’ummar kasar nan suka maida hankulan su a kan jerin sunayen na mutane 43.
PREMIUM TIMES HAUSA ta kalato ‘kabli-da-ba’adin’ da suka cukurkude sunayen wadanda majalisa za ta fara tantancewa a yau Laraba.
1 – RASHIN CIKA WA MATASA ALKAWARIN NADA SU MINISTOCI
Ranar 21 Ga Janairu, Daraktan Kamfen na Matasan APC mai suna Tony Nwoye, ya shaida a wani taro cewa sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari, kuma yay i musu alkawarin cewa a wannan zango zai nada matasa ministoci a cikin ministocin sa. Sai dai kuma yayin da sunayen suka fito, babu ko daya daga cikin matasan da suka yi wa APC fafutikar kamfen din zaben 2019 ko daya.
Isa Pantami ne mafi karancin shekaru 47 a cikin ministocin. Shi kuma ba ya cikin gurguzun matasan da suka taya Buhari jekal-jekalar kamfen tsawon shekaru da shekaru.
Mai bi masa a karancin shekaru 49, shi ne Festus Keyamo, wanda lauyan EFCC ne, daga baya kuma ya rikide ya koma tantarin dan siyasar kare akidar Buhariya. Kuma shi ne daraktan yada labarai na kamfen din Buhari a zaben 2019.
‘Yan wasan fina-fainan Hausa sun yi ta watsa bayanan cewa sun a sa ran za a ba fitaccen dan fim din nan Ali Nuhu mukamin ministan wasanni da matasa.
Ko a ranar da aka bayyana sunayen ministocin, sai da ka ga wasu ‘yan wasan sun je majalisa, sun a nuna goyon bayan su cewa a nada Ali Nuhu Minista.
2 – RASHIN SUNAN KABILUN YANKIN ABUJA NA NEMAN TAYAR DA KURA
Al’ummar asalin yankin Abuja da kewaye sun yi fatali da jerin sunayen ministocin da Shugaba Buhari ya fitar, a bisa dalilin cewa babu dan kabilar su ko daya a cikin sunayen. Wata sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Hadaddiyar Kungiyar Kabilun Abuja, Sumner Shagari-Sambo ya sa wa hannu a jiya Talata bayan fitar da jerin sunayen ministoci, ta ce sun gaji da zalunci da kuma danniyar da ake wa kalibun yankin Abuja.
Sun yi korafin yadda ake kwace musu kasasr su ta gado, ana bai wa wasu suna kantama-kantaman gine-gine ana kara mamaye su. Sannan kuma sun ce ba a taba nada dan asalin kabilar Abuja ministan Abuja ba.
Sun ce a yau za su dora wa Sanata Philips Aduda da ke wakiltar su, ya tashi a gaban majalisa ya nuna rashin amincewa da saka dan kabilar Abuja a cikin ministoci.
3 – ZARGIN NADA WADANDA APC TA YI WA ‘WANKAN TSARKI’
Jama’a da dama sun yi mamakin nada wasu da ake ganin cewa sun koma APC ne a lokacin da EFCC ke binciken su. Sannan kuma daga bisani kamar Timipre Sylva tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, sai da ya koma APC aka kori karar sa, sannan kuma aka maida masa da gidajen da aka kama.
Godswill Akpabio ya koma APC a lokacin da EFCC ke neman sama da naira bilyan 100 a hannun sa. Ya tsaya takarar sanata amma ya fadi. Yanzu an nada shi minista, kuma babu wata kotu da ta wanke shi. Wanda hakan ya jefa jama’a tunanin cewa ko dai mulkin Buhari ya yi adabo da akidar yaki da cin hanci da rashawa.
4 – NEMAN BAMBANCIN MAGE DA KYANWA
Makonni biyu da suka gabata, Buhari ya ce akasarin wadanda ya nada ministoci duk bai san sub a, ‘yan alfarma ne kawai. Amma a yanzu sai ya darje a cikin wadanda ya sani gar-da-gar. Kuma sai wadanda ya tabbatar da nagartar su.
Wannan ya sa jama’a na al’ajabin cewa shin irin su Silva da Akpabio ne ya sani gar-da-gar, kuma mutane nagari da ya tabbatar da nagartar su din kenan?
5 – NADA MAI HARKALLAR DABINON SAUDIYYA MINISTA
An cika da mamakin anin sunan Sadiya Faruk daga Jihar Zamfara ya sa jama’a da dama sun tuna da harkallar cinye tulin dabinon da kasar Saudiyya ta bai wa Najeriya tallafi a lokacin azumin bara, da niyyar raba wa jama’a, musamman a mazauna sansanin masu gudun hijira a lokacin shan ruwa.
6 – HADA KEYAMO DA SLYVA A WURI DAYA
Bayyana sunan babban lauya Festus Keyamo a cikin jerin ministoci, ya sa wasu da dama na gwasale gwamnatin Buhari. Idan ba a manta ba, Keyamo ne lauyan da EFCC ta dauka, ya gurfanar da Timipre Silva a kotu, akan zargin wawurar bilyoyin kudade. Ya yi ta kokarin nuna wa kotu irin gagarimar satar da y ace Sylva ya yi tare da gidajen da ya mallaka.
Bayan Sylva ya koma APC daga PDP, sai Keyamo ya fito ya ce ya tsame hannun sa daga gurfanar da Sylva, saboda wasu mishkilolin da ya ke fuskanta da wasu uzurorin da suka hana shi ci gaba da aikin.
Ba a dade ba kuma sai aka wanke Sylva ta hanyar maida masa da gidajen sa da EFCC ta kwace.
A yau Silva da Keyamo duk ministoci ne, za su rika zama a kan teburi daya ana gudanar da ayyuka, a matsayin sun a ministoci nagari da Buhari y ace zai darje kafin ya nada.
7 – RASHIN DAWO DA WASU MINISTOCIN KAN MUKAMAN SU
Jama’a da dama sun yi farin ciki jin cewa Buhari bai sake nada wasu ministoci da dam aba. Cikin wadanda aka yi murnar rashin sake komawar sa akwai Mansur Dan-Ali tsohon ministan tsaro.
A zamanin sa rashin tsaro yay i muni a jihar sa, wato Zamfara. Cikin kananan hukumomin da kashe-kashe suka yi kamari, har da Birnin Magaji, inda nan ne aka haife shi.
Sai kuma tsohon ministan ayyukan gona Audu Ogbeh, wanda sau da yawa an fi kuka da shi wajen yawan shekaru da kuma tsufa. Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa wasu lokuta idan zai hau bene sai an rike shi, don kada yay i tangal-tangal ya fadi, ko ya rikito kasa.
Shi ma Abdur-Rahman Dambazau an sha yin kuka da shi cewa a matsayin san a ministan harkokin cikin gida, muggan makamai sun shigo cikin kasar nan, wanda mallakar su ta kara haifar da hare-hare da kashe-kashe sosai musamman Arewa.
Tsohon Ministan Harkokin Lafiya, Isaac Adewale ma ba a ji haushin kin nada shi da Buhari ya yi ba.
Duk da kusancin da ake ganin Solomon Dalung na da shi ga Shugaba Muhammadu Buhari, hakan bai sa an maida shi a matsayin minista ba.
Ana ganin daga cikin dalilan har da wata dala dubu 13, 000 da ya kasa maida wa Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa.
8 – TULIN TSOFFIN ’YAN ALEWA A CIKIN MINISTOCIN BUHARI
A cikin ministocin da Buhari ya bada sunayen su, akwai tsoffin gwamnoni har guda 9 da kuma tsoffin sanatoci su bakwai. Sannan kuma akwai wadanda suka taba yin wakilci a Majalisar Tarayya na zango daya ko sama da haka.
9 – KORAFIN RASHIN YIN RABA DAIDAI
Dokar Najeriya ta ce shugaban kasa zai zabi ministocin sa daya daga kowace jiha a cikin jihohin kasar nan. A baya ministocin sa 36 ne. A yanzu kuma 43.
Maimakon a ce an kara minista daya daga kowace shiyya, sai a ka kara ministoci biyu a Shiyyar Arewa maso Yamma. Wato aka zabo minista biyu a Jihar Kano da kuma Jihar Kaduna, wadanda a shiyya daya suke.
Hakan ya sa wasu na ta korafin cewa an yi wa yankunan su rashin adalci.