Rundunar ‘yan sanda ta gabatar da mutane 13 dake da hannu a sace Magajin Garin Daura

0

Rundunar ‘yan sanda Najeriya ta gabatar da mutane 13 da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da aka yi da Magajin garin Daura Musa Umar a watan Mayu.

A ranar daya ga watan Mayu ne wasu masu garkuwa da mutane suka arce da Magajin Garin Daura Musa Umar.

Masu garkuwan dauke da bindigogi sun waske da Magajin Gari ne yayin da yake zaune a kofar gidansa bayan ay dawo sallan Magriba tare da jama’a.

Bayan kwanaki 60 yana tsare wajen masu Garkuwan ‘Yan sanda suka ceto sa daga hannun su. Sun kama wasu, wasu kuma sun arce da rauni a jikkunasu.

Jami’in hurda da jama’a na rundunar Frank Mba ne ya sanar da haka da yake gabatar da masu garkuwa da mutane da wasu ‘yan bata gari 27 ranar Litini a hedikwatan ‘yan sanda dake Guzape Abuja.

Mba yace sun kama wadannan mutane ne tsakanin jihohin Katsina da Kano.

“ Wadanda aka kama suna hada da Dahiru Yusuf mai shekaru 20 kuma shine shugaban kungun wadannan masu garkuwa, Aminu Saleh, mai shekaru 46; Abdullah Mohammed mai shekaru 26; Bilal Yusuf maishekaru 32 da Sarfilu Abdu mai shekaru 25.

“Sauran sun hada da Dahiru Musa mai shekaru 38; Tukur Bukar mai shekaru 35; Ibrahim Ibrahim mai shekaru 26; Mohammed Saidu mai sherkaru 36; Abubakar Adamu mai shekaru 27; Mustapha Zakariyya mai shekaru 32; Ibrahim Mohammed mai shekaru 29 da Bako Mustapha, mai shekaru 29.

Bayan haka ‘Yan sanda sun kwato rigunan sojoji, manyan bidigogi, na’ura mai aiki da kwa-kwalwa wanda ke dauke da bayanan yadda ake hada bama-bamai, da mugan makamai.

Mba yace ka kara da cewa masu garkuwan sun shaida wa ‘yan sanda cewa sune suka yin garkuwa da mafi yawan turawan da ke aiki a kamfanonin dake wannan yanki.

Shi ko gogan masu garkuwan, Dahiru Yusuf ya ce babban dalilin da ya sa suka arce da magajin gari sannan suka tsare shi shine don su jawo hankalin jam’ian tsaro a sako musu ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da.

Sannan kuma wasu daga cikin masu garkuwan dake tsare sunce baya ga neman a sako ‘yan uwansu kamar yadda Dahiru ya bayyana, sun yi garkuwa da Magajin Gari Umaru ne saboda a biya tulin kudin fansa. Sun ce suna sa ran samun akalla dala miliyan 30.

Bayan haka Mba ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada kai da jami’an tsaro ganin cewa dana gida ake hada baki domin a ci gari.

Ya kuma yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta karfafa dokar hana aikata miyagun aiyukka kamar su sace sacen mutane da dabobbi a kasar nan.

Share.

game da Author