Rikicin Boko Haram ya kara kassara jama’a daga Oktoba 2018 – UN

0

Kwamitn Majalisar Dinkin Duniya Mai Lura da Kungiyoyi a Jihar Barno, Adamawa da Yobe, ya bayyyana cewa rikicin Boko Haram da ake fama da shi yankin ya kara yin kamarin da tilas dimbin jama’ar da rikicin ya shafa daga watan Oktoba zuwa yau, su na bukatar a kai musu daukin gaggawa.

Kwamitin wanda ya kunshi manyan jami’ai daga Kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin sa-kai na NGO, ya bayyana haka ne a Abuja, bayan ya kammala ziyarar kwanaki biyar da kawo Najeriya.

Sanarwar da kwamitin ya fitar ta kara nuna matukar damuwa da kakkausan jan-hankali cewa jama’ar da ke fama da rashin abinci a yankin sun karu da kashi 10 bisa 100 tun daga cikin watan Oktoba 2018, zuwa yau.

“A yayin wannan ziyara, wadannan manyan jami’ai sun yi ganawa da Ma’aikatar Kasafin Kudi d Tsare-tsare, Gwamnan Jihar Barno da kuma kungiyoyin bada agaji da na UN da ke gudanar da ayyukan jinkai a Maiduguri.

‘‘Sun kuma ziyarci sansanonin masu gudun hijira da dama. Tare kuma da kai ziyara wasu garuruwan Boko Haram ya fi yi wa mummunar barna. Sun ziyarci garuruwan Damboa, Dikwa da Rann a Jihar Barno.”

Sanarwar ta hakaito Daraktar Gudanar da Shirye-shirye ta Ofishin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (UNCHA), Reena Ghelani na cewa: “A gaskiya matsalar da Yankin Tafkin Chadi ke ciki, ta na nan daram, babu wata alamar kawo karshen matsalar.”

“Mun hadu da mata da kananan yara wadanda suka rika ba mu labarin yadda hare-haren Boko Haram ya rika tilasta su tserewa daga nan zuwa can. Bayan dan lokaci kuma a kara kai musu hari, su sake tsarewa daga nan zuwa can. Wadannan mutane su na bukatar abinci, kulawa, tsaro da kuma duk wani tallafi da za su samu domin gina sake gina rayuwar su.

“Milyoyin jama’a a wannan yanki na bukatar agaji da tallafi daba gare mu. Don haka ba za mu bar su har kunci ya kayar da su, su kai gargara ba.

“Mun kuma ci karo da wasu masu dimbin yawa da suka shafe shekaru da dama su na zaune a sansanonin masu gudun hijira.

“Suna bukatar abinci, kuma za mu yi kokarin tallafa musu da ko da dan abin da za su samu kananan sana’o’in dogaro da kai ne su rika yi domin sake gina rayuwar su.”

Wakilin Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Edward Kallon, ya bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin Najeriya da sauran kamfanoni masu zaman kansu su hada hannu da UN domin a samar wa wadannan milyoyin al’umma madafar tashi daga kassarawar da Boko Haram ya yi musu.

“Duk da irin ajali da tallafin da ake bayarwa wanda ke ta karuwa a kwanan nan, duk da haka mu na damuwa matuka da ganin yadda wasu dubban mutane da suka gudu daga hare-hare kwanan nan ke kwana a tantagaryar tsandaurin kasa, a fili.”

Sanarwar ta nuna cewa ganin yadda damina ta shigo a yanzu, to wadannan duban jama’a masu kwanciya a waje za su fuskanci kamuwa da cututtuka da kuma barazanar rashin tsaro.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta nemi tallafin gudummawar dala milyan 848 daga masu hali, domin gudanar da ayyukan ceto rayuwar mutanen da suka tagayyara kimanin milyan 6.2 a cikin 2019.

Amma a watanni shida da suka gabata, UN ta ce ta samu kashi 36 bisa 100 na adadin kudaden da ta ke bukata domin aiwatar da wannan gagarimin ayyukan agaji.

UN ta ce akalla mutane milyan 7.1 ne ke matukar bukatar tallafin ceto rayuwar su daga kunci da tagayyara.

Share.

game da Author