Abu ne sananne a Najeriya, matasa masu shaidar karatun HND, digiri, har da Masters suna rayuwa cikin fatara da talauci bayan kammala bautar kasa.
Wannan shaharren abu ne a kasar mu, amma wasu suna ganin hakan yana da alaka da rashin adalcin da yake kasuwar samun aiki (Labour market).
Saidai wasu kuma suna gani kamar rashin samar da kyakykyawan yanayi ne da matasa zasu iya tsayawa da kafarsu.
Wasu kuma suna gani kamar talaucin matasa yana da nasaba da buri da suke dashi a rayuwarsu duba da yadda da yawancinsu basa yin karamar sana’a.
Gaskiya kowanne daga ciki zai iya zama dalili amma abun da mutane masu rinjaye suka yadda dashi yana da alaqa da rashin daidaito (equality) a kasuwar daukar aiki.
Misali, a kasar Najeriya ne ‘dan talaka zai gama jami’a da sakamako na daya (first class) amma ya shekara uku babu aiki saboda bashi da kowa sai Allah.
A bangaren wasu masu muqami a cikin gwamnati kuwa zaka samu matashi ya gama jami’a da mummunan sakamako amma tun kafin ya gama an ajje masa gurbin aiki.
Wannan shahararren abu ne a Najeriya, don ana samun wasu tun daga jami’a suke sanin irin ayyukan da za a basu idan sun kammala karatu. A lokacin da ‘dan talaka mai sakamako mai kyau yake yawo duk takalmansa sun mutu saboda neman aiki.
Da yawa daga cikin irin wadannan matasan suna cikin kuncin rayuwa da fatara saboda sun zama ci-ma-zaune bayan kammala karatu kafin shigowar tsarin Npower, kuma ba lallai bane su iya aikin karfi saboda buri irin na ‘graduates’ din Najeriya.
An dade ana neman hanyoyin da za abi don warware matsalar rashin aiki a Najeriya. Babban abun da yake bayar da mamaki shine, za kaji ana cewa babu aikin yi, mutane sun yi yawa, kaza-da-kaza, amma gashi kuma samun aikin babu wahala a wajen wasu.
Misali, duk sanda ‘yar wani babban mutum ta jarabtu da son ‘dan talaka sai a kirashi cikin gaggawa a bashi aiki mai kyau don ya riqe masa ita da kyau.
Wannan dalilin ne yasa ‘ya’yan talakawa yin auren jari saboda neman mafita. Gasu nan da yawa a Kano, Kaduna da Abuja, kullum fatansu shine, Allah ya hadasu da ‘yar wani Pharm Sec, DG, Senator, Minister ko wani babban dan kasuwa.
To menene mafita ga Najeriya da wadannan matasa?
Na farko, yakamata gwaunati ta gane cewa, duk gwamnatin da ta kasa samar da daidaito a cikin bayar da dama ga mai rabo (equality of job opportunities), gaskiya tana da matsala.
Na biyu, sai dukiyar Najeriya tayi tasiri a rayuwar talaka, ta hanyar samar masa da hanyoyin da zai rayu ba tare da gwamnati ba, a samar da hanyoyi na gaske.
Na uku, dole sai an samu hanyoyin wayarwa da matasan Najeriya kai don su gane cewa, shi fa aikin gwamnati na mai rabo ne (privilege), su yi amfani da iliminsu wajen samarwa da kansu aikin yi.
Abu na hudu, ina bawa matasa shawara, su ci gaba da neman ilimi, kada jikinsu ya mutu don suna ganin ‘yan uwansu sun yi karatu basu da aikin yi. Tabbas, rashin ilimi yafi rashin aiki zama kalubale. Tunda sai da ilimi dan Adam yake rayuwa cikin ‘yanci da mutunci. Kuma duk abun da zai zagi mai ilimi, lallai kai jahili idan yazo kanka kasheka zai yi.
Allah ya shiryar damu.