Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya yi kira ga kasashen duniya da su maida hankali wajen kiyaye yin allurar rigakafi a kasashen su.
Kungiyar ta yi wannan kira ne bayan binciken da ta yi tare da hadin guiwar asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) a 2018.
Sakamakon binciken ya nuna cewa har yanzu akwai akalla yara miliyan 20 da ko ba suyi alluran ba ko kuma ba su yi duka allurarn ba.
WHO ta ce cututtukan da ya kamata a fi maida hankali wajen yin allurar rigakafin su sun hada da bakon dauro, amai da gudawa da na dafin tsatsa ‘Tetanus’.
“Binciken ya nuna cewa matsayin da duniya take game da yin allurar rigakafin wadannan cututtuka ya kai kashi 86 bisa 100 wanda kamata ya yi an wuce haka.
Kasashen da rashin zaman lafiya ya hana su iya kammala yin rigakafi ga ‘ya’yan su sun hada da Afghanistan,jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya,jamhuriyar Kongo, Ethiopia, Haiti, Iraq, Mali, Nijar, Najeriya, Pakistan, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan, Syria da Yemen.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban WHO Adhanom Ghebreyesus yace rashin yi wa yaran wadannan kasashen duniya allurar rigakafi na sa a dade ana fama da matsalolin kiwon lafiya a kasashen.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne ne wasu kwararrun ma’aikatan fannin kiwon lafiya suka yi kira ga kasashen Afrika da su mai da hankali wajen ganin sun inganta yin allurar rigakafi a kasashen su.
Kwararrun sun yi wannan kira ne a taron inganta yin allurar rigakafi da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) na yankin kasashen Afrika ta yamma ta shirya.
Shugaban taron Helen Rees ta ce bincike ya nuna cewa yin allurar rigakafi a kasashen Afrika na nan a kashi 72 bisa 100 shekaru biyar da suka gabata.
Discussion about this post