Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani magidanci mai suna Tijjani Yahaya mai dake da shekaru 57 da laifin daba wa dan-uwansa Aminu Muhammed mai shekaru 20 wuka a kirji.
Jami’in hurda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna ya sanar da haka wa manema labarai a garin Kano.
Haruna ya ce wannan tsautsayin da abin tausayin ya faru ne ranar 19 ga watan Yuli da karfe tara na dare a makarantar islamiyar Annandin dake Kofar Ruwa a karamar hukumar Dala.
Ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa Yahaya ya caka wa dan uwansa wuka ne a kirji a dalilin musu da ya kaure a tsakanin su.
Yanzu dai kwamishinan ‘yan sadan jihar ya bada umarnin aci gaba da tsare Yahaya har sai an kammala bincike akai.
Dan uwan nasa, wato Aminu ya rasu bayan an kaishi asibiti.
Idan ba a manta ba kwanakin baya ne Mariya Suleiman, ‘Yar shekara 19 ta caka wa wanta Sani Suleiman wuka a ciki a wajen bukin ‘Ya yan su a Kano, kawai don basu samu jituwa ba wajen wakar da za a saka a wajen rawa.