A dalilin matsanancin rashin cibiyan kiwon lafiya a kauyen Wuro Ahmadu dake Gongoshi, karamar hukumar Mayo-Belwa, mazauna sun maida masallacinsu asibiti.
Ardo Buba, wanda shine shugaban wannan kauye, ya ce bayyana cewa mazauna wannan Ruga na fama da matsanancin rashin asibiti.
” Abisa wannan dalili yasa muka hakura mu ka maida masallacinmu tilo guda daya asibiti, domin kula da marasa lafiya.
” Sai anyi tafiya mai tsawo kafin nu cimma asibiti. Hakan na sa mutanen mu da dama na fadawa cikin halin kaka-nikayi idan babu lafiya.
Yayi kira ga gwamnati da ta taimakawa al’umman wannan kauye da magunguna da kuma inganta cibiyar.
Buba ya ce akalla mutane 1000 ne ke zama a wannan kauye sannan suna da shanu da dabbobi sama da 20,000.
Ya roki gwamnati da ta gina musu makarantu da asibitoci domin ilimin yaran su da.
Game da ruwan sha kuwa, ya ce gidauniyar CZ Cusson sun gina musu rijiyoyin butsatse masu aiki da hasken rana har guda biyu domin jama’ar su.