Obasanjo yayi tir da kisan ‘Yar shugaban kungiyan Yarabawa

0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya aika wa iyalan shugaban kungiyar Afenifere Rueben Fasoranti sakon ta’aziyar rasuwar ‘yarsa da masu garkuwa suka kashe a Akure.

Obasanjo ya yi addu’ar Allah ya ji kanta kuma ya ba iyayenta da ‘yan uwa hakurin jure wannan rashi da sukayi.

Bayannan ya ya yi kira ga gwamnatoci da na tarayya da a maida hankali wajen ganin an kawo karshen hare-haren makiyaya da ya addabi kasar nan.

Obasanjo ya aika da sakon sa ta hannun tsohon gwamna Yerima Oyinlola Ogunseye, kafin har ya dawo daga kasar Morocco.

Idan ba a manta ba ranar Juma’ a ne Kungiyar Yarabawa na Afenifere ta sanar cewa masu garkuwa sun kashe ‘Yar shugaban kungiyar Reuben Fasoranti a hari da suka kai wa motar su.

Kakakin kungiyar Yinka Odumakin ya bayyana cewa Funke Olakunrin, mai shekaru 58 ta rasu ne bayan wasu masu garkuwa dauke da bindigogi sun bude wa motan da take ciki wuta.

Wani da abun ya faru a idonsa ya ce Fulani ne suka tare motar a hanyarsu na zuwa garin Ore daga Akure.

Sun harbi Olakunri da hakan yayi sanadiyyar rasuwarta.

Masu garkuwan sun tattare wasu motocin.

Share.

game da Author