Najeriya ta gano hanyoyin kudaden shiga 22 da za su maye gurbin danyen mai

0

An bayyana hanyoyi 22 da gwamnatin tarayya za ta iya samun kudaden shiga wadanda za su iya maye gurbin kudaden da ake samu ta hanyar cinikin danyen mai a kasuwannin hada-hadar duniya.

Shugaban Hukumar Karfafa Kayan Kasuwannin Waje, Segun Awolowo ne ya bayyana haka.

Awolowo ya yi wannan bayani ne a ranar Juma’ar da ta gabata ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan kammala ganawar da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai kuma Awolowo bai bayyana wa manema labarai wadannan hanyoyi 22 da ya bugi kirji da su ba.

Amma dai ya shaida musu cewa ya fayyace wa Shugaban Kasa hanyoyin da za a bi domin fadada tattalin arzikin kasa ta hanyar kara samun makudan kudaden shiga. Ya ce dukkan abin da ya shaida masa, su na cikin tsarin da kwamitin fadada tattalin arziki da Majalisar Inganta Tattalin Arziki ta Kasa ta kafa.

An kafa wannan kwamiti na musamman ne a karkashin shugabancin gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru. Kuma an ba su nauyi da lahakin lalubo hanyoyin samun kudaden shiga wadanda ban a dogoro da danyen man fetur ba.

Awolowo ya kara da cewa duk da farashin danyen mai ya kara kudi a kwanan nan, kuma danyen man shi ne kashi 90 bisa 100 na hanyar samun kudin shiga ga Najeriya, to Najeriya ba za ta iya dogara da danyen man fetur shi kadai ba. Ya ce tilas sai an nemo wasu hanyoyin samun kudin shiga domin inganta tattalin arzikin kasar nan.

“Tilas sai gwamnati ta kara lalubo hanyoyin samun kudaden shiga. Domin lokacin da farashin gangar danyen man fetur ya kai dala 140, ya shude, har abada an wuce wurin. Don haka tilas sai mun kara nemo wasu hanyoyin samun kudade.” Inji Awolowo.

“Mu na da wasu hanyoyi 22 na samun kudaden shiga ga gwamnatin tarayya, ba tare da dogaro da danyen mai ba. Don haka mu na fatan nan da shekaru 10-15. Za mu iya samun akalla dala bilyan 150 daga wadansu hanyoyin kudaden shiga da ba hanyar cinikin danyen man fetur ba.”

Daga cikin wasu hanyoyi da Awolowo ya bayyana, akwai shirin da Babbban Bankin Tarayya (CBN) ke yi domin bayar da lamuni ga manoman da za su rika noma kayan amfanin noma masub kawo ribar kasuwanci irin su cocoa, kashu, tumatir da sauran su.

Share.

game da Author