Tsohon ministan kimiya da Fasaha Obonnaya Onu ya bayyana cewa Najeriya na amfani da dabarun gargajiya domin sarrafa maganin cutar dajin dake kama nono da cutar kuturta.
Onu wanada sunan sa na cikin jerin sunayen ministocin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wa majalisar dattawa domin tattancewa ya fadi hakane a zauren majalisar ranar Laraba.
Kafin ya zama minista Onu ya yi gwamnan jihar Abia sannan a lokacin da yake ministan ma’aikatar ta fara gudanar da bincike kan magungunan gargajiya domin gano manin da zai warkar da wadannan cututtuka.
Ya ce har yanzu dai ma’aikatar nan kan gudanar da bincike ganin cewa bincike irin haka kan dauki dogon lokaci kafin a samu ingantaccen magani.
“ A Mafi yawan lokutta binciken da ake gudanarwa a kasarnan bincike ne wanda mutum kan yi domin samun karin girma a wajen aiki kawai.
“A maimakon haka kamata ya yi duk binciken da za a gudanar ya zama bincike ne da kasar za ta iya mora.
Bayan haka sanata Sam Egwu ya yi wa Onu tambaya game da bacewar tauraron Dan Adam din Najeriya a sararin samaniya inda Onu ya bayyana cewa babu tauraron da ya bace saidai wadanda suka lalace aka gyara.
Daga nan sai majalisar ta sallami ya kama gabansa.