NAFDAC ta tabbatar da ingancin ruwan roba na ‘Eva’

0

Bayan kammala bincike hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta tabbatar da cewa ruwan roba, mai suna ‘Eva Premium Table Water’ na da inganci.

Shugaban hukumar Mojisola Adeyeye ce ta sanar da haka a shafinta ta Tiwita.

“Sakamakon binciken da muka gudanar a kan wannan ruwa da kamfanin ‘Eva Premium Table Water’ ke yi a Asejire, Ibadan jihar Oyo ya nuna ruwan na da tsafta.

“ Mun kuma dauki matakan da za su taimaka mana wajen sa ido a wannan ruwan domin tabbatar da cewa mutane na shan ruwa mai tsafta daga wannan kamfani.

Mojisola ta yi kira ga mutane da su ci gaba da shan ruwan.

A makon da ta gabata ne hukumar NAFDAC ta dakatar da aiyukkan kamfanin ruwan roba mai suna ‘Eva Premium Table Water’ dake kauyen Asejire a jihar Oyo kan rashin amincin ruwan.

Mutane sun yi ta kai kukan su ga hukumar game da rashin ingancin wannan ruwa cewa zaka rika ganin datti-datti a cikin ruwan sannan wataran ma har canja kala zaka ga yana yi.

“Tabas wannan kamfanin ruwa ta yi rajista da mu kuma duk ta san sharuddan da ke kunshe a cikin takardar da suka karba.

“Wadannan sharudda kuwa sun hada da sarrafa ruwan da bashi da kala, baya wari sannan babu datti a ciki.

NAFDAC ta ce kamfanin zata iya ci gaba da ayyukanta tunda an gane tsaftar ruwan.

Share.

game da Author