NAFDAC ta dakatar da kamfanin sarrafa ruwan leda a jihar Bauchi

0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta dakatar da aiyukkan kamfanin sarrafa ruwan leda mai suna ‘Ummi Table Water’ dake Azare a karamar hukumar Katagum jihar Bauchi.

Jami’in hukumar Abubakar Jimoh ya sanar da haka ranar Asabar.

Jimoh ya ce hukumar ta dakatar da wannan kamfanin ne a dalilin rashin yin rajista da ita.

“Mun gano zaman wannan kamfani ne yayin da muke gudanar da bincike a jihar.

Ya kuma ce hukumar ta kuma rufe kamfanin sarrafa ruwan leda mai suna ‘T-Cee Table Water’ dake nan a Azare.

Jimoh yace sun kama wannan kamfani ne da laifin yin amfani da na’urar sarrafa ruwa mara aminci.

Ya ce NAFDAC za ta ci gaba da aiyukkan ta tuƙuru domin tabbatar da cewa mutane na amfani da ingantattun magunguna da abinci da ake sarrafa su daga kamfanoni masu aminci a kasar nan.

Share.

game da Author