MINISTOCI: Kungiyoyin Rajin Dimokradiyya sun yi tir da sake nada Malami

0

Gamayyar Kungiyoyin Rajin Inganta Dimokradiyya da ‘Yancin Jama’a, sun yi tir da ganin an sake nada tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami a cikin sabbin ministocin da Buhari ya mika sunayen su a Majalisar Dattawa.

Tuni tun ranar Juma’a ne Majalisar Dattawa ta tantance Malami wanda kuma shi ne tsohon Antoni Janar na Tarayya.

Kungiyoyin da suka hada da AFRICMIL, YIAGA, CISLAC, CTA, LAWNAC, PAACA, P2P, CODE da kuma CISA, sun jaddada cewa sake dawo da Abubakar Malami a cikin ministoci ya kara tabbatar da cewa ikirarin yaki da cin hanci da rashawa ya zama tatsuniya kawai.

Malami, wanda a lokacin tantance shi aka tambaye shi dalilin da ya sa gwamnatin Buhari ba ta bin umarnin kotu a lokacin da ya na Ministan Shari’a, ya bayyana cewa gwamnati ba ta sakin wanda kotu ta bada umarnin a saki, matsawar ta na ganin sakin sa wata barazana ce ga tsaron kasa.

Musamman tambayoyin da aka yi masa da kuma amsar da ya bayar, su na bayani ne a kan rashin sakin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kuma Sambo Dasuki, wadanda ke tsare tun cikin 2015.

Kungiyar ‘Transparency International’, ta ce rashawa da cin hanci ba su ragu ba a zamanin Abubakar Malami na Ministan Shari’a tsakanin 2016 zuwa 2019.

“Irin yadda Malami ya rika shirya harkallar biyan wasu lauyoyi dala milyan 15 a matsayin kamashon ladar maido wa Najeriya kudaden da Abacha ya sace, bai kamata a ce ya sake zama minista a Najeriya ba.”

Shi kuwa Shugaban Kungiyar CISLAC, Rafsanjani, ya ce yanzu haka akwai wasu dala milyan 500 da Abacha ya kinshe a Amurka, amma Amurka ta ce muddin Malami ne ministan shari’a, to ba za ta dawo wa Najeriya da kudin ba.”

Shi ma daya daga cikin shugabannin gangamin kungiyoyin, mai suna Jaye Gaskia haka ya bayyana.

Rafsanjani ya ce ministocin da Buhari ya bada sunayen su alama ce mai nuna cewa an saki layin yaki da cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa kowa ya dora tunanin cewa da aka zabi Buhari a 2015, za a ga wani gagarimin sauyi kan yaki da cin hanci da rashawa.

Amma sunayen da Buhari ya mika a matsayin sabbin ministocin sa, ya nuna cewa batun yaki da cin hanci da rashawa ya zama tatsuniya kawai.

Share.

game da Author