Matsayin mu a kan El-Zakzaky da ‘yan Shi’a – Majalisar Dattawa

0

Sanata Betty Apiafi, wadda mamba ce a Kwamitin Yada Labarai da Kafofin Sadarwa, ta bayyana cewa bukatar da mabiya Shi’a ke yi ta a saki jagoran su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ta fi karfin hurumin Majalisar Dattawa.

Ta yi wamman bayanin ne a lokacin da mambobin wannan kwamiti suka yi wa manema labarai jawabi a Majalisar Dattawa, jiya Laraba.

Tawagar wadda Shugaban Kwamitin Adebayo Adeyeye ya jagoranta, sun yi bayanin ne biyo bayan hargitsin da ya faru a ranar Talata, lokacin da masu goyon bayan a saki El-Zakzaky suka kutsa cikin Majalisa da karfin tsiya.

Mabiya malamin sun yi zanga-zanga a kofar shiga Majalisa, wadda a karshe ta yi muni, har aka yi wa wasu jina-jina.

Adeyeye ya ce mafusata sun ci karfin jami’an ntsaron da ke tsare kofar shiga Majalisa, wadda aka fi sani da ‘MOPOL Gate.’

Daga nan sai ya yi kira da a kamo dukkan wadanda ke da hannu wajen gudanar da hargitsin da ya faru.

Ya kuma yi kira da a kara yawan jami’an tsaro a Majalisa.

Yayin da aka yi masa tambaya dangane da korafin da mabiya El-Zakzaky suka rubuta wa Majalisar Dattawa, sai Adeyeye ya ce sun rubuta korafin ne ga Majalisa wadda zangon ta ya kare cikin watan Mayu, 2018, ba wannan sabuwa da ta fara aiki a watan Yuni ba.

“Idan su na so Majalisa ta saurare su, ai ba da hargitsi za su shigo ba. Su rubuto mana takarda, su nemi a zauna da su. Sai a aika musu ranar da za su turo wakili daya ko biyu da za mu zauna da su mu tattauna.”

Sanata Betty kuma ta ce majalisa ta tattauna batun ci gaba da tsare El-Zakzaky da kuma rikicin da ke faruwa a majalisa dalilin tsare shi. Sai dai ta yi karin hasken cewa a ba zauren majalisa ne a ka tattauna batun ba.

“Mun yi kokarin shiga tsakani domin samun maslaha. Mun sha zama da kwamiti na Majalisar Tarayya a kan wannan batu. Amma ina ganin yadda mabiyan sa ke daukar lamarin, ba ita ce hanyar da ta fi dacewa ba.

“Za su iya turo wakilan su a koda yaushe domin mu zauna da su. Mu ma mu na taya su jimamin da suke ji na tsare jagoran na su. Mu na kuma sane da akwai wasu hukunce-hukunce biyu da kotu ta yanke a kan batun. Abu ne wanda ya fin karfin mu.” Inji ta.

Share.

game da Author