MATSALAR TSARO: Yari yayi wa Obasanjo ta-tas

0

Duk da cewa a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara rashin zaman lafiya ya ƙazanta a jihar, AbdulAziz Yari ya caccaki tsohon shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo game da matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita.

Yari ya ce ba irin Obasanjo bane zai riƙa fitowa yana sukar gwamnatin Buhari musamman idan maganar taɓarɓarewar tsaro za ayi a ƙasarnan.

” Kowa ya sani cewa a Obasanjo ne da kansa ya aika aka dirkake mutanen Odi a jihar Bayelsa da Zaki Biam a jihar Benue. A lokacin Obasanjo ne aka yi rikicin Kaduna inda aka rasa rayuka da dukiyoyi masu ɗinɓin yawa.

Yari ya ƙara da cewa a lokacin Obasanjo na shugaban Ƙasa, Jos babban birnin jihar Filato ita ma ta faɗa halin ƙaƙanikayi na rashin zaman lafiya da tsaro.

” Sannan kuma ko ya manta cewa a karkashin mulkin sa ne aka kashe Bola Ige da kuma Harry Marshal.

Ya kara da cewa a iya binciken da yayi ya gano cewa wasu ne suke amfani da siyasa domin rarraba kan ƴan Najeriya.

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya sake rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasiƙa, inda a wannan karon ya gargaɗe shi cewa Najeriya ta kama hanyar shiga bala’in ‘katilan-makatulan’, kuma Buhari ɗin ne kaɗai zai iya hana ƙasar faɗawa cikin wannan mummunan bala’i.

Obasanjo ya ce kashe-kashe da rikice-rikice na ci gaba da zame wa Najeriya bala’i, ga kuma babbar matsalar yadda ƙabilanci ya ruruta wuta tun bayan hawan Buhari mulki, shekaru huɗu da suka gabata.

Obasanjo ya ce an shafe shekaru masu yawan gaske rabon da Najeriya ta samu kan ta cikin irin wannan masifa da ake fama da ita.

Idan ba a manta ba, cikin wasiƙar da ya rubuta masa, ya shaida wa duniya cewa Najeriya fa ta kamo hanyar afkawa cikin kashe-kashen da idan ba a yi da gaske ba, to zai yi wuya a iya kashe gobarar.

Share.

game da Author