Hukumar UNFPA na majalisar dinkin duniya ta yi kira ga gwamnatocin duniya kan yin amfani da shirin ICPD da aka tsara domin inganta kiwon lafiyar mata a duniya.
A 1994 a Cairo kasar Masar ne aka tsara wannan shiri domin tallafa wa mata a kasashen duniya 179 dake fama da matsaloli wajen haihuwa.
Jami’in UNFPA Eugene Kongnyuy yace sai dai tun da aka tsara wannan shiri shekaru 50 da suka gabata mata daga wadannan kasashe basu rabu da fama da matsaloli wajen haihuwa ba.
Sakamakon binciken ya nuna cewa mata miliyan 1.6 da ‘yan mata 2.3 a Arewa Maso Gabashin Najeriya na bukatan tallafi matuka wajen haihuwa.
Hakan na da nasaba ne da addabar wannan yanki da Boko Haram suka yi ta yi a lokutta da dama.
Bayan haka sakamakon binciken ya kara nuna cewa a yanzu akwai mata miliyan 214 a duniya dake fama da karancin dabarun bada tazaran iyali.
A dalilin wannan matsala kuwa ya sa a kullum ake rasa mata 800 a duniya sannan a Najeriya mata 111 ake rasawa duk saboda matsalolin da sukan yi fama da a wajen haihuwa.
Adadin yawan mutane a duniya bai ragu ba domin sakamakon bincike ya nuna cewa adadin yawan mutane ya karu a duniya daga biliyan 3.6 a 1969 zuwa biliyan 7.7 a 2019.
A Najeriya kuwa adadin yawan mutane sun karu daga miliyan 140.4 a 2006 zuwa miliyan 198 a 2018.
Discussion about this post