Babban Basaraken Yarabawa kuma Ooni na Ife, Adeyeye Ogunwusi da Wole Soyinka, sun bayyana kakkausan gargadi ga gaggan ‘yan siyasar kasar nan cewa su dauki matakan da suka kamata wajen yayyafa wa cacar-bakin da ke ta faruwa a kasar nan ruwan sanyi.
Fitattun Yarabawan biyu sun yi nuni da cewa idan ba a kauce wa irin wannan tarangahumar ba, to ta na iya haddasa yakin basasa a kasar nan.
Daga nan sais u biyun suka ce a yanzu kuwa Najeriya ba za ta iya juriyar shanye dafin yakin basasa ba, irin yadda ta jure tsakanin 1967 zuwa 1970.
Su biyun sun yi wannan kira ne a cikin wata takardar bayan taron da suka sa wa hannu bayan tashi taron da suka yi a Idi Aba, Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Idi Aba can ne mahaifar Wole Soyinka a jihar Ogun.
Sun yi karin bayanin cewa irin yadda ake rura wutar kiyayya a tsakanin juna, zai iya haddasa mummunar barna a tsakanin rayukan ‘yan Najeriya. Sannan kuma ya na kara zama babbar barazana wajen kasancewar Najeriya kasa daya al’umma daya.
Masu Kwakwazon kafa rugage Kidahumai ne
Soyinka da Ooni na Ife, sun bayyana ra’ayoyin su dangane da tsarin da aka nemi shigo da shi na kafa wa Fulani makiyaya rugage a jihohin kasar nan, cewa tsari ne na “yi wa jama’a wani salon mulkin mallaka”, wanda wasu kidahumai kuma marasa ci gaba suke kokarin tabbatarwa.”
Sanarwar ta ce babban basaraken ya kai wa Soyinka ziyara a garin haihuwar sa ne domin nuna damuwa da tattauna matsalolin yadda ake ruruta wutar kiyayya da karin rabuwar kawunan kasar nan tare kuma da matsalar rashin tsaro.
“Wannan kasar Najeriya, wadda dama can Turawan mulkin mallaka ne suka dunkule mu a wuri daya, ba mu ne mu ka dunkule kan mu ba, to ba za ta iya jure wani sabon yakin basasa bamai kama da irin yadda yankin Biafra ya nemi ballewa. Domin yakin basasa tarwatsa ta zai yi.
Sun fito karara sunn lissafa cewa matsalolin Boko Haram da makiyaya masu hare-hare na daga cikin manyan matsalolin da ke bukatar magancewa a cikin gaggawa a kasar a halin da ake ciki a kasar nan.
“Mu na sane kuma mu na ji, mu na ganin yadda Fulani makiyaya da uwar kungiyar su ta Miyetti Allah ke gugumarar tarwatsa tsarin zamantakewar mu.
“Mun kuma fito fili mun sanar da irin yadda mu ke fama da takaicin yadda aka wayi gari ake neman a tarwatsa tsarin zamantakear rayuwar mu, ta hanyar rashin maida hankali ko kuma hadin guiwa da masu dauke da makamai wajen kakkabe manoman mu da ke samar mana da abinci da kuma kayann abincin da ke samar wa al’umma kudaden shiga.
“Irin wannan mummunan kashe-kashe da ake yi wa wani bangare da gayya, ba wai kawai ya na maida kasar nan baya wajen iya dogaro da kan ta ba ne, rashin imani ne, babban laifi ne kuma shiri ne na raba kan kasar nan.”
Sun kara da cewa wannan matsala da ake fama da ita, ba sabuwa ba ce, domin a baya ma an fuskance ta. Amma abin takaici ga bangaren gwamnarti, ta na gani ba za ta yin wani hobbasa ba, har sai bayan jama’ar da abin da dama ko ya shafa sun nuna rashin amincewa ko fushin su tukunna.
DA MAHAUKACINKA ZA KA YI MAGANIN MAHAUKACIN WANI
“A nan, mun yarda cewa kasassabar da jinsin kabilar wata kungiya ta yi, inda ta bada shuagaban kasa wa’adin sake dawo da shirin kafa Ruga, duk kuwa da al’ummar kasar nan sun ce ba su yarda ba, mun amince cewa sun yi gargadin ne saboda su na da ‘yancin bayyana ra’ayin su.
“Don haka mu ma muna yin kira ga daukacin ‘yan Najeriya a fadin jihohin su da su kare kasar su ta gadon-gado. Domin kasar haihuwar ka ita ce shaidar asalin ka, wadda hatta ma Turawan mulkin mallaka ba su kwace wa kowa ta sa ba.”
Discussion about this post