Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Ya ku jama’ah! Yana da kyau da matukar muhimmaci mu fahimci asalin Sarauta, masarautun mu da Sarakunan mu na Musulunci na kasar Hausa. Domin fahimtar su da sanin su za ya sa mu san matsayin su a cikin al’ummah, wannan sai yasa mu girmama su, kuma mu san darajar su.
Su dai wadannan masarautu namu da dukkanin tsare-tsaren su, ya kamata mu san cewa ba turawa bane ko mulkin mallaka ko mulkin soja ko tsarin dimokradiyyah ya samar da su a Nijeriya.

Masarautun sun girme wa dukkan wadancan tsare-tsaren da na ambata. Kuma wadannan masarautu tsari ne na Musulunci ya samar da su, sanadiyyar gwagwarmayar Musulunci domin tabbatar da Shari’a da ya faro tun daga shekarar 1804, wadda ita ce ta samar da Cibiyar Daular Usumaniyyah, mai dauke da Masarautu 33 kamar yadda masana tarihi suka shaida muna. Shehu Usman Dan Fodio, a matsayin sa na babban malami, mujahidi, shine ya jagoranci sauran malamai da dalibai a wannan gwagwarmaya, aka yi jihadi, da Allah ya basu nasara sai aka tabbatar da wadannan masarautu, wanda shi Shehu shine Amirul Mu’minina ko Sarkin Musulmi. Shine ya bai wa wadannan Sarakuna tuta suka zama Amirai, wato shugabannin Musulunci a masarautun su, shi kuwa shugaba wato Shehu, yana Birnin Sakkwato. Haka fa wadannan masarautu da sarakuna bayin Allah suka ci gaba da gudanar da sha’anin Musulunci da warware matsalolin al’ummah har zuwa yau da nike wannan rubutu. Bisa la’akari da ilimin tarihi, za mu ga cewa wadannan masarautu an samar da su ne tun shekaru dari kafin turawa suyi wa Nijeriya mulkin Mallaka.
Wadannan masarautu namu na Musulunci, masu daraja, tun lokacin da aka kirkiri kasar Nijeriya suke ta shan wahala, suke ganin wulakanci da musgunawa a wurin makiya Musulunci da Musulmai, wato turawan mulkin mallaka, da ‘yan koren su daga cikin wasu sojoji da ‘yan siyasa. Saboda haka, maganar rarraba masarautar Kano da tsatstsaga ta da Gwamnatin Ganduje ta yi a yau, wanda kuma In Shaa Allahu, mun san cewa sai an rusa su, kawai ci gaba ne da wancan aiki na makiya Musulunci da Musulmai, da kuma rarraba kan jama’ah da kokarin haifar da husuma, adawa da gaba tsakanin al’ummah; kuma wannan yunkuri ne na rusa tsarin dukkanin masarautu a Kano da kuma ko’ina a arewacin Nijeriya.
Ya ku jama’ar Musulmi! Wannan kadan kenan game da bayani akan asalin wadannan masarautu namu. Kuma rashin sanin wannan ko jahiltar wannan ko kuma son zuciyar mu shine yake sa kaga Musulmi Dan arewa, abun mamaki, wai yana kokarin cin mutuncin masarautun mu, ko kuma ka ga mutum Musulmi Dan arewa, wai yana goyon bayan wani Dan siyasa domin tozartawa tare da cin mutuncin wani Sarki daga cikin sarakunan mu na Musulunci.
Kamar yadda na ga wasu shedanun ‘yan siyasa da magoya bayan su, suke kokarin yin batanci ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, akan yayi kokarin ya bayar da shawarwari masu amfani ga gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, a wurin taron da ofishin Babban Akawun Tarayyar Nijeriya ya shirya a Birnin Kano. A wurin wannan taro, shawarwari Mai Martaba Sarki ya bayar, a matsayin sa na masanin tattalin arziki, ya yabawa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a inda ta kyautata, ya bata shawara a inda ya kamata tayi gyara.
Amma sai miyagun mutane, shedanu, masu kokarin haddasa husuma da fitina tsakanin shugabanni, domin cimma wani buri na su, suka yi kokarin juya wadannan jawabai na Mai Martaba, a matsayin wai yana attacking gwamnati ne.
Alhali duk mutum mai ilimi, mai basira, idan ya kalli jawabin Sarki ko ya karanta shi, za ya ga cewa wallahi babu inda Sarki yayi attacking shugaba Muhammadu Buhari ko gwamnatin sa.
Jaridu irin su The Nation da sauran kafafen yada labarai na yanar gizo, da sauran kafafen yada labarai na zamani duk sun ruwaito cewa wai, Mai Martaba Sarki yana cewa, “KASAR NIJERIYA NA DAB DA DURKUSHEWA” wato NIGERIA ON THE VERGE OF BANKRUPTCY”, wanda wannan kawai sharri ne da kage da karya ga wannan bawan Allah, wato Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
Bayan wannan sharri da makarkashiya na kokarin canza kalaman Sarki ya wuce, wanda munafukai da makirai da magauta basu ci nasara ba, sai kuma kwatsam muka ga miyagu, ciki har da jam’iyyar APC ta Jahar Kano, da masu yi masu kamfen a kafafen yada labarai na zamani, irin Facebook, WhatsApp da sauransu, suna ta yada hoton Mai Martaba Sarki tare da ‘yar sa Husnah Sanusi, wadda Sarki ya halarci bikin yayen ta a makarantar su da ke Birnin Ikko, wato Legas, tare da rakiyar Damburan, Alhaji Munir Sanusi (Shugaban ma’aikatan fadar Kano).
Da yake mu a nan Nijeriya muna da saura a wayewa da ilimi, wai yau an wayi gari mutum ya nuna wa ‘yar sa da ya haifa soyayya da kauna ta hanyar kara mata karfin gwiwa a karatun ta, ya zama wani abun tsegumi, abun surutu, abun cece-kuce da hayaniya! Wai jahilcin mu har yasa wasu suna ganin bai kamata Mai Martaba Sarki yayi haka da ‘yar sa da ya haifa ba!
To ku sani, babu wani laifi da Sarki yayi a nan. Mai Martaba yayi daidai, domin zamani ne yazo da haka, kuma Musulunci baya fada da abun da zamani ya kawo, matukar abun nan bai sabawa Musulunci ba. Idan Sarki yabi zamani bai yi laifi ba!
Idan ku baku jawo ‘ya ‘yan ku a jika, idan ku baku nunawa ‘ya ‘yan ku kauna da soyayya shike nan sai kuyi ta zama a haka, amma kar ku zama kidahumai, wawaye, ku sa wa wani ido idan kun ga yayi hakan!
Sannan daga karshe, abun da nike so mu fahimta a wannan makala tawa shine, rashin sanin muhimmacin masarautun mu shi yasa da wani Sarki daga cikin Sarakunan mu yayi wani abu sai kaji ana ta kokarin cin mutuncin sa da nuna masa raini. Sannan abun mamaki, Sarakunan nan fa ya kamata mu fahimci cewa, su ba ma’asumai bane, wato ba Annabawa bane, kuma su ba Mala’iku bane. Mutane ne kamar kowa, amma sai dai banbancin mu da su, su shugabannin ne da Addinin Musulunci ya wajabta muna yin biyayya gare su. Dole ne muyi masu da’a, sai fa idan sun umurce mu da aikata abun da yake ya sabawa Allah da Manzon sa!
Saboda haka kar mu dauka cewa su ma’asumai ne basu yin laifi, sai wannan yasa mu sa masu ido a cikin al’amurran su. Da sun yi abu kadan muyi ta yayata shi muna kokarin raina su!
Allah ya taimake mu, yasa mu dace, amin.
Dan uwanku,
Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nijeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.