Majalisar Dattawa ta tafi hutun makonni 8

0

Bayan bayyana sunayen shugabanni da mambobin majalisar dattawa da shugaban Majalisar Ahmaad Lawan yayi a Zauren ranar Talata, ya bayyana cewa majalisar za ta tafi hutunta na shekara-shekara na tsawon makonni 8.

Kafin rufe majalisar, Shugaba Lawan ya yabawa sanatocin bisa kokarin da suka yi na jurewa har a aka kammala tantance ministocin da shugaban kasa Mauhammadu Buhari ya aiko majalisar.

” Ina so in tabbatar muku da cewa wannan shine karo na farko da majalisa ta yi irin wannan namijin kokarin wajen ganin tunda ta fara aikin tantance ministocin sai da ta dire.

” Mun dakatar da hutun mu domin ganin an kammala wannan aiki. Abinda nake rokon wadanda za a nada dashi shine su kwana da shirin cewa zamu yia aiki ne tare domin ci gaban kasa. Majalisa zata rika bibiyan ayyukan su domin irin haka ginshikin ayyukan majalisa.

Ya roki ministocin da za a nada da su mara wa sanatocin baya a duk lokacin da suka bukaci yin aikin su.

Daga nan kuma sai ya bayyana cewa majalisar na sa ran fadar shugaban kasa za ta aiko da kasafin kudi na 2020 a watan Satumba ko kuma farkon watan Oktoba.

” Idan ko har aka aiko da kasafin Kudin a wannan lokaci, ina tabbatar muku da cewa zamu yi aiki akai sannan mu aika wa shugaban kasa cikin watan Disamba wanda iadan tayi wuta akai watan Janairu.

Share.

game da Author