MAIDUGURI: Yadda Boko Haram suka kutsa sansanin gudun hijira, suka yi kisa da satar abinci

0

Boko Haram sun yi wa sansanin ‘yan gudun hijira shigar-kutse suka kashe mutum biyu tare da satar kayan abinci.

Maharan kamar yadda majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar, sun kai harin ne a kan babura dauke da manyan bindigogi.

Lamarin ya faru ne a Sansanin Dolari da ke Maiduri, a jiya Alhamis wajen 8 na dare. Haka wani babban jami’an tsaro na sa-kai, wato CJTF ya tabbatar wa PREMIUM TIMES.

Abba Aji ya ce maharan sun kutsa cikin sansanin ne kan su tsaye ta kofar bayan wayar da ke kewaye da sansanin.

“Kafin su shiga ciki sai da suka fara kai hari a kan sojojin da ke gadin sansanin, daga nan kuma suka rika bude wuta a cikin sansanin.

“Sun kashe wani namiji daya da kuma karamin yaro. Sannan kuma duk da sojojin da ke gadin sansanin, Boko Haram sun fasa kantuna suka saci abinci, kuma suka fita kan su tsaye”

Aji ya ce wannan abin takaici ne kwarai da gaske, ganin yadda irin haka ke faruwa a wannan lokaci a Maiduguri.

Shi ma Babban Jami’in Tsaro da ke tare da Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Barno, mai suna Bello Dambatta, ya tabbatar da wannan hari, ya ce tabbas hakan ta faru.

Share.

game da Author