Mahara sun kashe direba daya, wasu shida sun ɓace a Barno

0

Mahara sun buɗe wa Jerin gwanon motocin bada agaji na ‘Action Againdt Hunger’da ke aikin bada agaji a jihar Barno ranar Alhamis a hanyarsu na zuwa garin Damasak.

Garin Damasak na kilomita 157 ne daga garin Maiduguri.

Koda yake abin ya faru ranar Alhamis ne, a yau Juma’a ne kungiyar ta fitar da bayanan abin da ya faru da ma’aikatanta.

Shaswat Sharaf wanda shine shugaban kungiyar a Najeriya ya ce motocin su dauke da ma’aikatan na hanyar su na zuwa garin Damasak ne aka far musu.

” Maharan sun buɗe wa motocin mu wuta inda suka kashe direba ɗaƴa sannan sauran direbobi biyu da ma’aikaran kiwon lafiya uku duk sun ɓace ba a san inda suke ba.

Sharaf ya ce wannan abu da ya faru ya tada musu da hankali matuƙa sannan yana fatan Allah ya sa wadannan ma’aikata nasu su bayyana domin komawa ga iyalan su.

Waɗannan mahara dai sunyi wa jerin gwanon motocin kwantan ɓauna ne inda kafin su isa wurin da suke su suka fara buɗe musu wuta.

Share.

game da Author