MAGUDIN ZABEN 2019: Amurka ta hana ‘yan siyasar Najeriya shiga kasar ta

0

Jiya Talata ne gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwar gaggawa cewa ta haramta wa wasu ‘yan siyasar Najeriya shiga kasar ta.

Ta ce ta ba za ta kara barin ta su shiga Amurka ba, saboda yunkurin sun a kokarin yi wa dimokradiyya kafar-ungulu a lokacin zaben 2019.

Amurka ta bada sanarwar ta ofishin Harkokin Kasashen Waje, cewa ta ware mutanen ne domin rawar da suka taka watanni biyar da suka gabata a lokacin zabe a Najeriya.

“ Wadannan ’yan siyasa sun shuka rashin mutunci matuka ta yadda suka tattaka dimokradiyya da kuma danne hakkin jama’a.” Haka Kakakin Yada Labarai na Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka, Morgan Ortagus ya bayyana.

Sai dai babu inda aka kama ko da sunan mutum daya daga cikin wadanda aka ce an haramta wa shiga Amurka.

Wani tsohon ma’aikaci a ofishin harkokin wajen Amurka ya shaida cewa tsarin boye sirrin kasar Amurka ya hana bayyana sunayen wadanda irin wannan haramcin shiga kasar ya shafa.

Sannan kuma ofishin na Amurka bai yi wata magana a kan sakamakon zaben ba, amma dai ya ce ya ware sunayen wasu ‘yan siyasa da suka yi kaurin suna wajen dagula zaben 2019 tare da tauye wa jama’a hakkin su.

Idan ba a manta ba, sai da Jakadan Amurka a Najeriya, Stuart Syminton ya yi kira ga masu zabe kada su bi umarnin da ba ya cikin hurumin dokar kasa, wanda wadansu za su fito da shi, da sunan umarni daga shugaban Kasa a lokacin zabe.

Sannan kuma kalamin da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi cewa duk wani dan kasar waje da ya yi wa zabe katsalandan, to za a maida shi kasar su a cikin jakar daukar gawa.

Daga bisani Buhari da El-Rufai sun nesanta kan su da furucin, inda El-Rufai ya ce ba a fahimce shi ba ne.

Share.

game da Author