Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon Kafa na Chelsea, Frank Lampard ya zama sabon Kocin kungiyar.
Idan ba a manta ba Tsohon Kocin kungiyar Sarri, ya canja Kulub zuwa kasar Italiya inda a kakar bana zai rike Kungiyar Juventus.
Kungiyar Chelsea ne ta lashe kofin UEFA a bara, karkashin Sarri.
A jawabin sa Lamdard ya ce ay yi matukar farinciki da dawowar sa Chelsea, yana mai cewa zai yi kokarin dawo da martabar kungiyar.