Lallai Majalisa ta binciki zargin cin Zarafin wata da Sanata yayi – Inji Uba Sani

0

Sanata Uba sani dake wakiltar Kaduna ta Tsakiya ya yi kira ga majalisar Dattawa da ta binciki badakalar cin zarafin wata da ake zargin Sanata Elisha cliff yayi a wani Shago a Abuja.

An kama Sanatan da ya fi sauran sanatoci mafi kankantar shekaru, ya na jibgar wata mata a cikin kantin da ake sayar da azzakarin roba da sauran kayan da mata ke jima’i da su na roba.

Lamarin ya faru ne a ranar 11 Ga Mayu, kafin a rantsar da su, a Abuja.

PREMIUM TIMES ta mallaki bidiyon yadda aka yi rikicin.

Sanata Elisha Abbo, wanda ya ke wakiltar Shiyyar Adamawa ta Arewa, ya hau matar da duka ne daga kawai ta je ta na ba shi hakurin kada ya doki mai tsaron kantin.

Sanata ya yi ikirarin cewa matar ta zage shi, shi ya sa ya hau ta da duka, kuma ta ce masa mashayin giya, bugagge wanda ya sha ya yi mankas.

Ya doki matar a gaban wani dan sandan mobal, wanda maimakon ya raba rigimar, sai ma ya yi kokarin kama matar.

An kai karar wannan fada a ofishin ‘Yan Sanda na Maitama, da ke kan titin Nile, amma sai suka ce sai an samo masu lambar sanatan kafin su iya yin wani abu tukunna.

Sanata Uba Sani ya ce wannan zargi na cin zarafin mace ya karde kasar nan kuma bai kamata ace majalisar dattawa ta yi shiru a kai ba. Kammala maganarsa ke da wuya sai shugaban majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya nada kwamiti domin bin diddigin wannan magana sannan su mika rahoton su a gaban majalisar nan da makonni biyu.

” Wasu daga cikin mu mun sadaukar da rayukan mu ne wajen kwato wa talakawa da marasa galihu hakki ne musamman Mata da yara. Ba zai yiwu ace irin haka na faruwa ba kuma a yi shiru ba. Ina kira ga majalisa da ta biddigin wannan abin tashin hankali da kunya.”

Share.

game da Author