Kungiyar Hisbah ta kama kwalayen giya 37, karuwai 48 a jihar Jigawa

0

Kungiyar Hisba a jihar Jigawa ta kama kwalayen giya 37 da karuwai 48 a karamar hukumar Taura.

Shugaban hukumar Ibrahim Daura ne ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata a garin Dutse.

Daura ya ce sun samu nasarar yin wannan kame ne bayan sun kai samame kauyen Gugunju tare hadin guiwar da rundunar ‘yan sandan jihar da suka bamu.

Ya ce sun kuma kama karuwai 30 da maza 18 duk a wannan kauyen.

Daura ya ce sun danka wadannan mutane ga hannun rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

Ya kuma yabawa taimakon da matasan kauyen suka ba su a lokacin da suka kai wannan samame.

” Muna kira ga mutane da su guji aikata miyagun aiyukka. Kungiyar Hisbah ba za ta yi kasa-kasa ba wajen kawar da masu aikata miyagun aiyukka kaf a jihar.”

“Muna kuma yi wa mutane tunin cewa shan giya da aikata miyagun aiyukka abubuwa ne da aka hana yin su a wannan jiha”.

Idan ba a manta ba, kwanakin baya kungiyar Hisbah a jihar Kano ta kama mata 11 da laifin shirya daurin auren mata biyu a matsayin mata da miji.

Wannan abin mamakin ya faru ne a Sabon Gari dake karamar hukumar Fagge.

Jami’in Hisba Nasiru Ibrahim ya sanar da haka inda ya bayyana cewa sun sami labarin haka ne daga bakin mutanen da suka san aiyukkan da wadannan mata ke yi.

” Mun sami labarin cewa ana daurin auren wasu mata biyu da Safiyya Yobe da Fatima Gezawa a Sabon gari.

Ibrahim yace jin haka ke da wuya suka gaggauta zuwa Sabon gari inda suka kama mata 11 cikin su da mata biyu da ake bunkin daurin auren su a matsayin mata da miji.

Share.

game da Author