Kudirori 17 da Buhari ya ki amincewa su zama doka

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da wasu kudirori 17, wadanda Majalisar Tarayya zango na 8 da ta shude ta aika masa domin ya sa musu hannu su zama doka.

Amma kuma ya sa wa wadansu kudirorin 9 hannu sun zama doka.

Babban Hadimin Shugaban Kasa a Harkokin Majalisar Dattawa, Ita Enang ne ya bayyana haka a jiya Laraba wajen wani taron da ya shirya da manema labarai.

Sai dai kuma ya ce Buhari ya yanke shawarar cewa ba zai aika wa sabuwar Majalisar Dattawa wannan zango na 9 wasika a kan kudirorin da ya ki sa wa hannu ba, domin ba za su yi wani abu a kan su ba.

Amma kuma Inag ya ce zai tuntubi dukkan majalisun biyu, ta Tarayya da ta Dattawa, domin yi musu bayanin dalilin kin amincewar da Shugaba Buhari na rashin amincewar sa su zama dokoki.

Ya ce babu wani abu da majalisar yanzu za ta iya yi domin tilasta shugaban kasa sa musu hannu, domin doka ba ta ba su ikon yin hakan ba.

Daga cikin kudirori 9 da Buhari ya sa hannu suka zama doka, har da Dokar Gidauniyar ‘Yan Sanda, Hukumar FCT, Hukumar Inshora, Dokar Satar Fasaha da sauran su.

Akwai kuma dokar Hukumar Gudanarwar Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta FCT.

Daga cikin 17 wadanda Buhari ya ki amincewa su zama doka, akwai: Kudirin Jami’ar Adeyemi, Jami’ar Ilmi ta Jihar Kano, Jami’ar Alvan Ikoku, Jami’ar Ilmi ta Zari’a, Kudirin Dokar Kula da Dabbobi Marasa Lafiya da sauran su.

Kudirin dokar Hukumar Kula da Fina-finai ta Kasa da sauran su.

Share.

game da Author