Kotun Koli ta tabbatar wa Gwamnan Osun, Gboyega kujerar Gwamna

0

A ranar Juma’a ne kotun koli ta tabbatar wa gwamnan Osun Gboyega Oyetola da kujerar sa ta gwamman jihar.

Idan ba a manta ba, dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke ne kotun sauraron kararrakin zabe ta ce ya lashe zaben jihar Osun din a hukunciun farko.

Saida kuma APC ta garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci.

A hukuncin da ta yanke a wancan lokaci, kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yince cewa akwai mishkiloli a ciki.

Adeleke ya nausa kotun Koli domin bin hakkin sa. Saidai kash bata haifar mai da da mai ido bva domin kuwa a yau Juma’a kotun wanda Alkalai bakwai suka zauna, ta yanke cewa kotun daukaka kara ta yi daidai wajen soke hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe.

Cikin Alkalai bakwai da suka yi wannan zama, biyu basu amince da hukuncin ba.

Babban dalilin da ya sa Adeleke bai yi nasara a kotun ba shine wai don alkalin da ya karanta hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe Peter Obiora a ranar 22 ga wata Maris, bai saka hannu a wani takardar hujjoji da kotu ta amince da su ba a ranar 2 ga watan Faburairu, cewa wai a dalilin haka bai da iko ko hurumin yanke hukuncin rashin nasarar APC da yayi.

Share.

game da Author