Kotu za ta bayyana ranar yanke hukunci kan takardun shaidar sakandaren Buhari

0

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta bayyana cewa nan gaba za ta bayyana ranar da za ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar dangane da sahihancin takardar shaidar kammala sakandare ta Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ya yi amfani da ita wajen shiga takarar zaben 2019.

Kotun mai mambobi uku, wadda Mai Shari’a Atinuke Akomolafe-Wilson ke shugabanta, bayan ta saurari bayanai daga masu shigar da kara da kuma bangaren wadanda ake karar, ta ce za ta bayyana musu ranar da za a yanke hukunci, da zaran kotun ta kammala komai.

A lokacin zaman kotun na jiya Litinin, lauyan masu shigar da kara, Ukpai Ukairo, ya jajirce a gaba masu shari’a cewa Buhari bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa, idan aka yi la’akari da takardun shaidar zurfin ilmin sa.

Lauyan ya ce dalili ma na farko shi ne, Buhari bai manna satifiket din sa na shaidar kammala sakandare ba a fam din INEC mai lamba CF001 ba.

Lauyan ya kara hakikicewa cewa tunda tilas doka ta ce sai da wancan fam fin za a tantance dan takara, to Buhari bai gabatar da na sa fam din ba.

Sannan kuma ya kara jajircewa da cewa an shigar da karar a ranar 5 Ga Nuwamba, watau a cikin kawanakin wa’adin kwana 14 da doka ta ce a daukaka kara.

Ya ce shigar da karar ta su tun da farko ta samo asali ne tun daga 25 Ga Oktoba, 2018, ranar da INEC ta yi sanarwar wadanda suka cancanta tsayawa takara.

Daga nan sai ya roki kotu ta yanke hukunci ta hanyar wancakali da hukuncin Babbar Kotun Tarayya, wadda ta yanke cewa Buhari ya cancaci tsayawa takara.

Lauyan ya roki kotu ta yi amfani da tulin hujjojin da ya gabatar, ta soke takarar Shugaba Buhari, ta haramta zaben sa da aka yi na ranar 23 Ga Febrairu.

Ya ce bai ga dalilin da INEC za ta kyale Buhari ya shiga takara ba, saboda a cewar sa, bai mallaki cikakkun takardun shaidar kammala sakandare ba.

Wadanda Suke tababar Shaidar Sakandaren Buhari

Idan ba a manta ba, Kalu Kalu, Labaran Ismail da kuma Hassy Kyari el-Kuris, su ne suka maka Buhari da APC da kuma INEC kotu, inda suke kalubantar cancantar Buhari tsayawa takarar zaben 2019.

Sun maka shi kara a gaban Mai Shari’a na Babban Kotun Tarayya, Ahmed Mohammed, wanda shi kuma ya kori karar ta su a bisa rashin dalilin cancantar shigar da karar, kamar yadda ya yanke hukunci a baya.

Yayin da suka daukaka kara, sun bayyana wa Kotun Daukaka kara cewa Mai Shari’a na Babban Kotun Tarayya ta tafka kuskuren korar karar ta su, wadda ya ce wai ba ta da hurumi, saboda a karar da suka shigar a gaban sa, ba su kalubalanci sakamakon zaben ba, sai cancantar Buhari tsayawa takara kadai suka kalubalanta.

Akan haka suka roki kotu ta cire sunan Buhari daga cikin ‘yan takarar zaben 2019.

Sai dai kuma lauyoyin Buhari da na APC duk sun roki kotu ta yi biris da wannan roko na wadanda suka shigar da kara.

Shi kuma lauyan INEC, ya bayyana wa kotu cewa Hukumar Zabe ba ta wani zabi, sai bin umarnin duk hukuncin da kotun ta yanke kawai.

Share.

game da Author