Kotu ta yi watsi da karar kalubalantar zaben gwamnan Zamfara Bello Matawalle

0

Kotun sauraren kararrakin Zaben gwamnan jihar Zamfara ta yio watsi da karar da wasu ‘yan jam’iyyar PDP.

Alkalin kotun Fatima Zeberu ta yi watsi da karan da Shehu Ahmed, Nasiru Lawal, Ibrahim Mohammed, da Salihu Zurmi wanda duk yan jam’iyyar PDP ne suka gabatar a gabanta.

Alkalin Kotun Fatima ta yi watsi da karar ne bayan kin cewa komai game da karar da aka gabatar a kotun da hukumar zabe da jam’iyyar APC ba su yi ba.

Kotun koli ta tabbatar wa jam’iyyar PDP da kujerun gwamnati na jihar Zamfara bayan kin yin zaben fidda gwani da jam’iyyar APC bata yi ba.

Share.

game da Author