Kotu ta tsare Adama da ta nemi kwace mijin aminiyarta dake tsare mata shago a Kaduna

0

Kotun Shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Kaduna, ta bada umarnin a tsare matar da ta yi kokarin neman mijin aminiyar ta.

Mai Shari’a Murtala Nasir ya ce a tsare Adama Arabi har sai ta samu mai belin da zai ajiye naira 100,000 a kotu tukunna.

Adama wadda ita ma matar aure ce, an kuma tuhume ta da laifin shiga gonar da ba tata ba.

Alkali ya ce ta samo mai belin da zai iya gamsar da kotu cewa ba za ta gudu ta ki dawowa kotu domin ci gaba da shari’a a ranar 25 Ga Yuli ba.

Daga nan kuma Alkali Nasiru ya gargadi aminan su biyu kada su sake wata mu’amala ta hada su domin kada wani sabon rikici ko balli ya kara tashi.

Fatima Sulaiman ce ta maka aminiyar Adama Arabi kotu, ta hanun lauyan ta Musbahu Mustapha, wanda ya shaida wa kotun cewa da wadda su ke karar da kuma wadda ya shigar da karar a madadin ta, wato Fatima, duk aminan juna ne.

Fatima wadda ‘yar kasuwa ce, ta kan rika bai wa aminiyar ta Adama labaran sirri na dangane da matsalar zaman auren da ta keyi da mijin ta.

“Kawai ita kuma Adama sai ta rika amfani da wannan damar sanin sirrin da ake kwashewa ana fada mata, ta rika karakainar zuwa gidan Fatima a cikin shiga da take bayyana tubarrujin mace.

“Fatima ta na da kanti a Malali, sai Adama ta rika zuwa kantin ba tare da Fatima ta kira ta ba. Saboda kawai ta san cewa mijin Fatima na nan zauna a kantin wasu lokuta. Mu na da shaidun da suka tabbatar da haka.”

Haka lauyan Fatima wadda ta kai karar Adama aminiyar ta ya shaida wa kotu.

“Bayan da Adama ta yi dukkan kokarin da za ta yi domin ta karkatar da zuciyar mijin Fatima mai suna Sulaiman Jere zuwa gare ta, sai kuma ta rika watsa ji-ta-ji-ta cewa wai ya na zuwa wurin ta ya na ba ta hakuri, kuma ya na ce mata ya na son ta.

“Wannan kasassaba da Adama ta yi, ta keta Dokar Sashe na 174, 373, 158 da kuma ta 232 ta Jihar Kaduna, wadda aka kafa cikin 2002.

“Mu na rokon kotu ta yi wa Adama hukuncin da ya dace da ita, domin ta nayi wa Fatima barazana, kuma ta ci amanar da ke tsakanin su.” Duk inji lauyan Fatima.

Sai da kuma Adama wadda babu wani lauyan da ke kare ta, ta musanta dukkan zargin da ake yi mata.

Share.

game da Author