Kotu ta daure magidancin da ya riƙa lalata da agola a gidansa

0

Kotu a Ikeja jihar Lega ta gurfanar da Idowu Daniel mai shekaru 28 wadda malamin makarantar sakandare na ‘Anastasia Comprehensive Collage’ dake Abule-Egba Ikeja da aka kama da laifin yin lalata da dalibarsa mai shekaru 17.

Alkalin kotun Olufunke Sule-Amzat ta yi watsi da rokon sassauci da Daniel ya nema, ta yanke masa hukuncin zama a kurkuku har sai kotu ta kammala tattaunawa da sashen da ake gurfana da masu aikata laifuka irin haka.

Lauyan da ya shigar da karar Benson Emuerhi ya bayyan cewa Daniel dake zama a Abule-Egba ya aikata wannan ta’asa ne ranar 27 ga watan Yuni da karefe 9:25 na safe.

Ya ce Daniel ya danne wannan daliba ne da ajin da ake koyar da kimiyyar dabobbi na makarantar bayan lallabanta da ya yi ta shigo ajin.

Dokar jihar Legas ya bayyana cewa duk wanda aka kama da aikata laifi irin haka zai yi zama a kurkuku na tsawon shekaru 14.

Alkali Sule-Amzat ta dage shari’ar jar sai ranar 21 ga watan Oktoba.

Bayan haka kotun ta kuma sake gurfanar da Micheal Akintayo mai shekaru 49 bisa laifin yin lalata da agolarsa mai shekaru 13.

Alƙalin kotun Olufunke Sule-Amzat ta yanke hukuncin a daure Akintayo a kurkuku har sai kotun ta kammala tattaunawa da fannin da ake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka.

Sule-Amzat ta daga shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba.

Lauyan da ya shigar da karan Benson Emuerhi ya bayyana cewa Akintola ya fara danne agolarsa ne tun daga 2017 zuwa watan Afrilu 2019.

“Akintola ya fara ne da saka yatsar sa a gaban wannan yarinya sannan bisa ga bayanan da yarin ta bamu ta ce Akintola ya yi lalata da ita har a watan Mayu.

Share.

game da Author