Kotu ta bada umarnin a kamo shugaban hukumar Kwallon kafa ta kasa Amaju Pinick

0

Babban kotu dake Abuja ta bada umarnin a taso keyar shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa, Amaju Pinick.

Alkalin kotun maishari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce ta yanke wannan hukuncin ne ganin cewa shi Pinick ya ki bayyana a kotu duk da umarnin haka da ta bashi.

Ijeoma Ojukwu, ta ce dole a taso keyar sa ya bayyana a kotu a zama na gaba, wato ranar 28 ga watan Satumba.

Ana tuhumar Pinick da handame Dala Miliyan 8.4 a lokacin gasar kwallo kafa na cin kofin duniya a Brazil a 2014.

Sannan kuma ana tuhumar su da shirya gasar karya domin yin sama da fadi da wasu kudade da sunan wai sun yi amfani da su a wajen shirya wadannan wasanni.

Share.

game da Author