Kotu ta ba da belin sanata Abbo

0

A yau Litinin ne jami’an ’yan sanda suka gurfanar da Sanata Elisha Abbo a kotu, bayan zargin sa da aka yi da dad-dalla wa wata matar aure mari a cikin kantin saida azzakarin roba a Abuja.

An gurfanar da shi ne a Kotun Majistare da ke Zuba, dake Abuja.

Alkalin kotun ya umarce Abbo ya kawo mutane biyu da za su tsaya masa sannan ya biya naira Miliyan biyu.

Sai dai kuma duk da cewa ya roki wannan mata da ya rika daddalla wa mari a shago da ‘yan Najeriya, Abbo a kotu yaki amsa wadannan laifuka da ya bayyana karara a wannan bidiyo.

Abbo ya na wakiltar Shiyyar Adamawa ta Arewa ce. PREMIUM TIMES ce ta fallasa wani bidiyon da aka nuno shi ya zubar da kimar sa ta sanata ya rika zabga wa matar aure mari a kantin sayar da kayan mata.

An tabbatar da cewa Abbo ya je kantin sayar da azzakarin robar ne tare da wasu mata uku, wadanda aka tabbatar da cewa babu matar sa a cikin su.

Kakakin Yada Labarai na Rundunar ’Yan Sandan Abuja, Anjuguri Manzah, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda sun shigar da tuhuma a kan Sanata Abbo, bayan da suka kalli bidiyon da aka nuno shi ya na zabga wa matar mari har a cikin idanun ta.

An watsa bidiyon a ranar 2 Ga Yuli, 2019, kuma nan da nan ya game duniya, har aka rika yi wa sanatan tofin Allah-tsine.

Duk da cewa Abbo ya fito ya bayar da hakurin abin da ya faru, hakan bai hana ‘yan sandan Abuja gayyatar sa ba. Amma dai daga baya an bayar da belin sa bayan daukar wani dogon lokaci a hedikwatar su ta Abuja.

Share.

game da Author