KATANKATANA: Kotun Koli ta sabule wandon Dan Majalisar APC, ta daura wa dan takarar PDP

0

A yau Talata Kotun Koli ya tsige Dan Majalisar Tarayya Aliyu Modibbo. Kotun Daukaka Kara ta Yola ce ta halasta zaben Modibbo a karkashin jam’iyyar APC.

Sai dai kuma Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Yola. Ta amince da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke cewa dan takarar PDP ne ke da nasara.

Wannan katankatana ta zaben Karamar Yola ta Kudu ce, Yola ta Arewa da kuma Girei na Jihar Adamawa.

Kotun Koli ya ki amincewa da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke, wadda ta mika nasarar ga wani dan takara daban na APC mai suna Mustapha Usman.

Tun da farko a Babbar Kotun Yola, mai kara ya yi korafin cewa Modibbo na APC wanda aka bai wa Nasara a bai cancanci tsayawa takarar shiga zabe ba, domin bai kammala aikin bautar kasa ba, wato NYSC.

Mai kara ya ce har zuwa lokacin da aka yi zabe, Modibbo ya na aikin bautar kasa, bai kammala ba.

Sannan kuma mai kara ya gabatar wa kotu wasu wuraren da Modibbo ya baddala takardun sa wadanda ya damka wa INEC kafin zabe.

Babbar Kotu a karkashin Mai Shari’a Abdul’aziz Anka ya nuna cewa mai kara ya gabatar da hujjojin da ya gamsar da kotu cewa bai kamata APC ta tsaida Modibbo a matsayin dan takarar ta ba.

Daga nan sai ya zartas da hukunci cewa dan takarar da ya zo na biyu shi ne zai maye gurbin sa a matsayin wanda ya yi nasara.

Dan takarar PDP mai suna Jafar Suleiman ne ya zo na biyu da kuri’u 48, 476, shi kuma Modibbo da aka kwace daga hannun sa, ya samu kuri’u sama da 80, 000.

Wannan hukunci bai yi wa wanda ya zo na biyu dadi ba a zaben fidda-gwanin APC. Sai ya garzaya daukaka kara.

Kotun Daukaka Kara sai ta hukunta cewa Usman ne ya kamata ya maye gurbin Modibbo.

Daga nan shi kuma Modibbo sai ya garzaya Kotun Koli domin neman kada a kwace nasarar da ya yi.

Sai dai kuma ita Kotun Koli ta bayar da nasarar ce ga dan takarar PDP a zaben Majalisar Tarayya, wanda ya zo na biyu, ba gad an takarar zaben fidda-gwanin APC da ya yi na biyu ga zaben fidda-gwani ba.

Share.

game da Author